You are here: HomeAfricaBBC2021 03 09Article 1199962

BBC Hausa of Tuesday, 9 March 2021

Source: BBC

Joachim Low zai bar horar da Jamus bayan Euro 2021

Joachim Low, kocin tawagar kwallon kafar Jamus Joachim Low, kocin tawagar kwallon kafar Jamus

Joachim Low zai ajiye aikin kocin tawagar kwallon kafar Jamus, bayan kammala gasar cin kofin nahiyar Turai ta 2021.

Mai shekara 61, ya maye gurbin Jurgen Klinsman a matakin kocin Jamus tun 2006.

Tun farko yarjejeniyar Low za ta kare da hukumar kwallon kafa Jamus, bayan kammala gasar kofin duniya da za a yi a 2022 a Qatar.

Kocin Jamus Low ya tsawaita yarjejeniyarsa

Kocin ne ya yanke shawarar ajiye aikin ya kuma yi godiya ga dukkan gudunmuwar da aka bashi, kamar yadda Low ya fada wanda ya lashe kofin duniya a 2014.

Bayan da tawagar Jamus ta ci kofin duniya a Brazil, Low ya kai kasar wasan daf da karshe a gasar cin kofin nahiyar Turai a 2016 da Faransa ta karbi bakunci.

Daga baya ne kocin ya fuskanci kalubale, bayan da aka yi waje da Jamus a wasannin cikin rukuni a gasar cin kofin duniya a 2018.

Jamus tana rukuni na shida da ya kunshi Faransa da Hungary da kuma Portugal a gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a bana.

Za a buga wasannin tsakanin 11 ga watan Yuni zuwa 11 ga watan Yuli a gasar da ya kamata a buga tun 2020 amma cutar koran ta kawo tsaito.

Tawagar Jamus za ta fara wasan farko a fafatawar da za ta yi da Faransa ranar 15 ga watan Yuni a filin wasa na Allianz Arena da ke Munich.