You are here: HomeAfricaBBC2021 04 01Article 1221493

BBC Hausa of Thursday, 1 April 2021

Source: www.bbc.com

Jirgin yaƙin sojin saman Najeriya 'ya yi ɓatan dabo' a Borno

Na'urar da ke hango zirga-zirgar jirage da tuntuɓarsu wato radar ta kasa ganin inda wani jirgin rundunar sojin saman Najeriya ya shiga, a cewar sanarwar rundunar.

Jirgin yaƙin yana kan wani aiki ne na taimakon dakarun rundunar sojin ƙasa a jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar.

Daraktan yaɗa labarai na rundunar ya ce an daina jin ɗuriyar jirgin ne tun ƙarfe biyar na yammacin Laraba 31 ga watan Maris."

"Har yanzu babu wasu bayanai kan inda jirgin ya shiga ko dalilin ɓacewarsa, amma za mu sanar da al'umma da zarar mun gano wani abu," a cewarsa.

Aikin da jirgin ke yi wani ɓangare ne na ci gaba da yaƙi da ƴan ƙungiyar Boko Haram da ake yi.