You are here: HomeAfricaBBC2022 12 30Article 1687988

BBC Hausa of Friday, 30 December 2022

Source: BBC

Jiragen sama sun koma aiki tsakanin Addis Ababa da Mekelle

Iyalai na kuka tare da sumbatar hasumiyar filin jirgin sama da ke Tigray Iyalai na kuka tare da sumbatar hasumiyar filin jirgin sama da ke Tigray

Iyalai na kuka tare da sumbatar hasumiyar filin jirgin sama da ke Tigray a Ethopia, yayin da suka yi cincirindo don saduwa da 'yan uwansu da yaki ya raba su, bayan shafe wata 18.

Yanyin abin tausayin, ya biyo bayan dawo da zirga zirga r jirage a tsakanin babban Birnin ƙasar zuwa Mekelle.

Birnin wanda ke da yawan al'umma da ya kai 500, 000an yanke shi da sauran sassan duniya sakamakon mummunan yaƙin da ya bake tsawon shekara biyu, da ya janyo asarar rayukan masu yawa, da raba sama da mutum miliyan daya da 'yan uwansu.

Gwamnati da mayaƙan Tigray Liberation Front, suka saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a watan da ya gabata, wanda hakan ya bayar da damar jirin daukar fasinjoji komawa harkokinsu a tsakanin jihohin biyu.

tashar talabijin a Tigray mallakar mayakan Tigray, ta haska wani bidiyo da ke nuna matafiya na durƙusawa akan guiwoyinsu suna sumbatar ƙasan filin jirgin saman dake Mekelle.

Suna cikin Haka alamarin yake na yanayin ban tausayi a filin jirgin saman Bole na kasa da ƙasa da ke Addis Ababa, a lokacin da mutane ke tururwar neman j9irgin zuwa Tgray.

Tun bayan toshe layin waya, mutane masu yawa basa iya ji daga 'yan uwansu, sama da wata 18, wanda suka ɗauki laokcin na ƙaguwar da jin ko suna zaune a gida lafiya.

Cikinsu har da Kahssay Hailu mai shekaru 47, da ya rasa yadda zai yi a Addis Ababa tun bayan da ta zo birnin da 'yar ta, a lokacin da take shirin fara rubuta jarabawa.

A lokacin da Mrs Kahssay ke jira a filin jirgin sama na Tigray don hawa jirgin da zai je Mekelle, ta fadawa Reuters cewar "Anan nake da zama, an raba ni da miji na ɗana da na fi so".

"A lokacin da na samu labarin, jirgi zai dawowar zirga-zirga a tsakanin jihohin biyu, faɗuwa ƙasa na yi ina kuka."

Wata mata Nigsti Hailemariam mai shekaru 67 ta ce a lokacin da ta iso Addis Ababa, don taimakawa 'yar ta dake da ciki, haihuwa."Na zo nan ne don na ga 'yata da za ta haihu. Na taho ne da shirin in zauna tsawon mako biyu, kwai sai aka dakatar da komai. Yanzu ga shi an kai shekara ɗaya da rabi.

" Ina matuyƙar jin daɗi ganin yadda zaman lafiya ya dawo, ina farin cikin cewar yanzu zan iya komawa gida.

Yaƙi ya ɓarke ne bayan samun saɓani a tsakanin Prime minista Abiy Ahmed da mayaƙan Tigray dake kula da yankin.

Mr Abiy ya zargin dakarun Tigray da kai hari sansanin sojojin a wani yunkuri na hamɓarar da shi daga kan mulki.

Inda ya mayar da martani ta hanyar umartar kai wasu hare hare ta sama, tare da aikawada dakarun ƙasar don kwace yankin da dakarun Tigray din ke da ƙarfin iko a yankin.

Ƙungiyar hadin kan kasashen Afrika ne dai suka shiga tsakani, bangarorin biyu, don kawo ƙarshen rikicin, tare da dawo da sauran ababen more rayuwa a yankin na Tigaray.