You are here: HomeAfricaBBC2023 03 22Article 1735901

BBC Hausa of Wednesday, 22 March 2023

Source: BBC

Jihohi shida da suka koma hannun ƴan adawa a Najeriya

APC plus PDP na di major parties for Nigeria APC plus PDP na di major parties for Nigeria

Duk da cewa har yanzu ba a kammala bayyana sakamakon zaɓen jihohi 28 cikin 36 da aka yi a Najeriya ba a ranar 18 ga watan Maris, amma ya zuwa yanzu akwai wasu jihohi da ƴan adawa suka karɓe daga hannun masu mulki.

Zuwa yanzu jihohi shida sun koma hannun jam'iyyun adawa waɗanda suka haɗa da Benue da Cross Rivers da Kano da Sokoto da Plateau da kuma Zamfara.

Amma jiran tsammani a wasu jihohin da suka haɗa da Adamawa da Abia da Kebbi da Enugu ka iya ƙara yawan waɗannan jihohin da shida.

Samun nasara kan jam'iyyar da ke mulki a Najeriya wani abu ne mai cike da mamaki, masana na ganin babu ɗan hamayyar da zai iya ƙwace mulki da tazarar da ba ta kai ta kawo ba.

BBC ta yi nazari kan nasarar da waɗannan jam'iyyu suka samu da kuma dalilin samun nasarar ta su:

Zamfara

Jihar Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin da suka fuskanci matsaloli masu tarin yawa a Najeriya cikin ƴan shekarun nan.

Matsalar tsaro ta mamaye yankuna da dama na jihar, kashe mutane da satarsu domin karɓar kuɗin fansa dai da ya zama tamkar ruwan dare.

A wannan karon mutanen jihar sun zaɓi sabon gwamnan da zai jagorance su cikin shekaru hudu masu zuwa.

Dauda Lawal Dare na jam'iyyar PDP shi ne ya samu nasara a zaɓen da ya gudana, ya kuma doke gwamna mai ci Muhammadu Bello Matawalle da ya nemi wa'adi na biyu bai samu ba.

Nasarar Dauda ana mata kallon zakaran da Allah ya nufa da cara.... ganin cewa mafi yawan ƴan siyasar Zamfara a ƙarƙashin inuwa ɗaya suke.

Kano

A jihar Kano ma sauyin jam'iyya mai mulki aka samu, inda jam'iyyar NNPP ta samu nasarar ƙwace mulki daga hannun APC mai mulki.

Abba Kabir Yusuf ne ya samu nasara a zaɓen da ya gubata .

Sai dai jam'iyyar APC da ta sha kashi a zaɓen a wani taron manema labarai da ta kira ta ce ba ta yarda da sakamakon zaɓen ba.

Jihar Kano ita ce jihar da ta fi kowacce yawan al'umma da kuma masu kaɗa kuri'a a arewacin Najeriya.

Sokoto

Jihar Sokoto da ke shiyyar arewa maso yammacin Najeriya ma ta yi sabon zaɓaɓɓen gwamna - Alhaji Ahmed Aliyu, wanda ya yi takara ƙarƙashin jam'iyyar APC.

Ya samu nasara ne kan abokin hamayyarsa na PDP, Sa'idu Umar wanda gwamna mai ci Aminu Waziri Tambuwal ya tsayar.

Jihar Sokoto ma na cikin jihohin da ke fuskantar matsalolin tsaro waɗanda suka ƙi ci suka ƙi cinyewa, kuma sabon gwamnan zai fuskanci wannan ƙaluable domin kawar da ita.

Plateau

Caleb Mutfwang shi ne zaɓaɓɓen gwamna a jihar Plateau, kuma ya yi takara ne ƙarƙashin jam'iyyar PDP mai adawa.

Ya doke ɗan takarar gwamna na APC, Nentawe Yilwatda wanda shi ne ɗan takarar gwamna mai ci Simon Lalong.

Masana na ganin cewa APC na fuskantar koma baya a jihar ta Plateau, ganin cewa ko a lokacin da aka yi zaɓen shugaban kasa da gwamnan jihar ya jagoranci yaƙin neman zaɓensa a Najeriya APC ba ta samu nasara ba.

Jihar Plateau ta yi ƙaurin suna wajen rikicin addini da ƙabilanci, a baya-bayan nan kuma an fara fuskantar satar mutane domin karɓar kuɗin fansa.

Benue

Rabaran Hyacinth Alia na jam'iyyar APC ne ya lashe zaɓen gwamnan jihar Benue da aka gudanar a ranar Asabar, wata nasara da masana suka bayyana a matsayin mai cike da tarihi.

Ya samu nasara ne daga hannun jam'iyyar PDP mai mulki, wadda gwamna Samuel Ortom zai kammala wa'adinsa na biyu a cikin watan Mayu.

A Benue ana fuskantar rikici na makiyaya da manoma, wanda kuma har yanzu yana cikin ƙalubalen da zaɓaɓɓen gwamnan Hyacinth Alia zai fuskanta a lokacin mulkinsa.

Cross Rivers

Karon farko tun daga 1999 da aka samu sauyin jam'iyya mai mulki a Cross River da ke yankin kudu maso kudancin Najeriya.

Tun lokacin da aka koma jamhuriya ta hudu a Najeriya, PDP ce ke jagorantar jihar.

Wannan ne karon farko da wata jam'iyya ba PDP ba, za ta jagoranci wannan jiha.

Bassey Otu shi ne hukumar zaɓen Najeriya INEC ta bayyana a matsayin wanda ya lashe zaɓen ranar 18 ga watan Maris da aka yi.