You are here: HomeAfricaBBC2023 01 30Article 1704818

BBC Hausa of Monday, 30 January 2023

Source: BBC

Jayayya tsakanin majalisun Najeriya da CBN kan wa'adin daina amfani da tsoffin kuɗin naira

Naira kudin Najeriya | Hoton alama Naira kudin Najeriya | Hoton alama

Majalisun Najeriya biyu sun ce suna nan a kan bakansu cewa sai babban bankin ƙasar ya ƙara wa'adin daina amfani da tsoffin takardun naira zuwa watan Yuni.

'Yan majalisar ta wakilai da dattawa, sun ce kwana goma da Babban Bankin ya ƙara sun yi kaɗan, kuma idan aka ci gaba da tafiya a haka mutane da dama za su talauce.

Tun da farko Babban Bankin ya ce tsoffin kuɗin da suka rage a hannun jama'a yanzu, ba su fi kashi 25 cikin 100 ba, kuma cikin kwana goma ana iya mayar da su bankuna.

Sai dai da alama waɗannan bayanai ba su gamsar da majalisun ba.

'Karin kwana 10'

Ahmed Bello Umar, daraktan hada-hadar kuɗi na Babban Bankin ya shaidawa BBC cewa a halin yanzu dai ba su hana kashe tsoffin kudi ba, kawai dai bankuna aka hana su fitar.

Sannan a cewarsa koken da jama'a suka rinka yi ne suka tursasawa shugaban kasa amincewa ko umartar a kara wa'adi da kwana 10.

Ahmed ya kuma shaida cewa yadda tsarin ya ke shi ne daga 1 ga watan Fabarairu zuwa 10 ga watan, ana sa ran jama'a su kammala sauya kudinsu a bankunan.

Sannan sauran kwanaki 7, wato daga 10 ga wata zuwa 17 ga watan Fabarairu, mutum na iya zuwa rassa Babban Banki da ke sassan daban-daban na kasar domin sauya kuɗinsu.

"Abin da mu ke son a gane komai ana yin sa ne saboda al'umma wannan ne dalilin da ya sa aka bijiro da hanyoyin da ake ganin zai saukakawa al'umma.

"Sannan a halin yanzu kashi 60 cikin 100 na sabbin kudaden da ake bukata akwai su, shi yasa aka kara kwanaki 10 wanda tabbas kafin nan kudin su wadata a fadin Najeriya.

"Ba mu isa mu yi komai ko yanke hukunci ba, ba tare da izinin shugana kasa ba, kuma ko a wannan lokaci shi ya bada umarnin a kara wa’adin karban tsoffin kudin," in ji Ahmed Bello.

Tunzura majalisa

Sanata Uba Sani wanda shi ne shugaban kwamitin kula da harkokin bankuna na majalisar dattijai, ya ce duk wadannan bayanai ba fa za su yarda ba a majalisa.

Kamar dai takwarorinsa a majalisar wakilai, Sanatan ya ce kwanaki 10 ya yi kadan, shi yasa suka yi kudirin da ya bukaci a tsawaita lokacin daina karban tsoffin kudaden zuwa watan shida na shekara ta 2023.

Sanata ya bada dalilansu kan karancin kuɗin da kuma talakawa mazauna karkara da kafin su dauko kuɗi zuwa inda akwai bankin lokaci zai kure musu.

Akwai kuma wadanda su kullum sun saba kuɗi na hannusu, shiyasa yake da bukatar a yi karin lokaci.

Sanata ya ce al'umma da suka zaɓe su, su tattauna da su, sun ji kukansu da illolin da hakan ya ke a garesu, shiyasa suka dage kan cewa dole a tsawaita lokaci zuwa watan Yuni.

Ya ce akwai bukatar su ma gwamnoni su tattara kansu baki ɗaya su zauna da shugaban kasa, domin tabbatar da cewa sun taimaka wajen nunawa Shugaban kasa girman matsalar don a sassauta.

Ya ce gwamnan Babban Banki ba ya yin abu shi kadai kai tsaye ba tare da umarnin shugaban kasa ba, don haka zama a fitar da matsaya ne kaɗai mafita.

Sanata ya gargaɗi cewa yin biris da bukatunsu da sauran al'umma da komai ake yi saboda su, na iya jefa mutane cikin talauci.

Shi ma jagorancin shugaban masu rinjaye na majalisar Alhassan Ado Doguwa, yana mai cewa dole CBN ya yi biyayya da sashe na 20, ƙaramin kashi na 3, da 4 da kuma 5 na dokar CBN.

Doguwa ya ce "Wa'adin kwana 10 da CBN din ya ƙara ba mafita ba ne, mu abin da kawai muke buƙata a matsayinmu na 'yan majalisa shi ne CBN ya yi biyayya ga sashe na 20 ƙaramin kashi na 3 da na 4 da kuma na 5 na dokar CBN''.

"A matsayin Najeriya na ƙasa mai tasowa, kuma mai bin tafarkin dimokradiyya dole mu yi biyayya da abinda doka ta tanadar.

Ya ƙara da cewa majalisar wakilan za ta bayar da umarnin kamo gwamnan Babban Bankin domin tilasta masa bayyana a gaban kwamitin.

Doguwa ya ci gaba da cewa kwamitinsa zai ci gaba da aiki har sai ya tabbatar da biyan buƙatun 'yan ƙasar kamar yadda doka ta tanadar.

Yayin da yake bayyana ƙarin wa'adin kwana 10 da cewa ba wani abu ba ne illa yaudarar 'yan ƙasar tare da ƙara jefa tattalin arzikin ƙasar cikin halin ni-'yasu, Doguwa ya ce dole ne gwamnan Babban Bankin ya bayyana a gaban Majalisar wakilan ko kuma ya fuskancoi barazanar kama shi, ta hanyar yin amfani da ƙarfin da doka ta bai wa majalisar.

Karin haske

Gwamnatin Najeriya dai tun da farko ta ce ta yanke hukunci sauya kudin kasar ne domin yaki da cin hanci da Rashawa.

Wata sanarwa da shugaba Muhammadu Buhari ya fitar na cewa akwai wasu mutane da suka yi amfani da mukamansu wajen boye kudaden kasa, kuma an gano wasu rubabun kudade da aka binne a karkashin kasa.

Shi ma Babban Bankin Najeriya CBN ya ce bayanan alƙaluman da yake da su sun nuna cewa ya zuwa watan Octoban 2022 yawan kuɗin da ke ɓoye a hannun mutane a ƙasar ya kai naira tiriliyan biyu da biliyan 700.

Gwamnan CBN ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su zama masu biyayya da haɗin kai wajen tabbatar an gama mayar da kuɗaɗen ba tare da wani tashin hankali ba.