You are here: HomeAfricaBBC2023 02 23Article 1720082

BBC Hausa of Thursday, 23 February 2023

Source: BBC

Jami'an tsaro sun kama jagoran a-ware na Biafra a Finland

Simon Ekpa, ya yi kira ga jama'a a yankin kudu maso gabashin Najeriya Simon Ekpa, ya yi kira ga jama'a a yankin kudu maso gabashin Najeriya

Hukumomin tsaro a ƙasar Finland sun damƙe fitaccen jagoran 'yan a-ware na Biafra da ke neman ɓallewa daga Najeriya, Simon Ekpa, wanda ya yi kira ga jama'a a yankin kudu maso gabashin Najeriya, da kada su fita zaɓen shugaban ƙasar da za a yi ranar Asabar 25 ga watan nan na Fabarairu.

Bayanai sun nuna cewa kafar yaɗa labarai ta ƙasar ta Finland inda jagoran ke zaune, Helsingin Sanomat ta ce wakiliyarta ta je gidan Ekpa domin yin hira da shi a ranar Alhamis 23 ga watan Fabarairu 2023, kamar yadda ya amince, sai ta ga jami'an tsaro na ƙoƙarin tafiya da Ekpa daga gidansa.

Bayanai sun nuna cewa jami'an tsaron ba su amsa wa wakiliyar tambayar da ta yi musu ta sanin dalilin kama shi ba.

A saƙonni da dama da yake sanyawa a shafin Twitter, jagoran 'yan tawayen ya jima yana kira ga jama'a a yankin kudu maso gabashin Najeriya da kada su fita ranar zaɓe, tare da barazana ga duk wanda ya bijire wa kiran, ya fita zaɓe, cewa zai gane kuskurensa.

An kama ɗan-a-waren ne, 'yan kwanaki bayan da gwamnatin Najeriya ta gayyaci jakadiyar ƙasar ta Finland a Najeriya, Leena Pylvanainen a kan barazanar da Epka ɗin ya yi kan yunƙurin haifar da matsala ga zaɓen na 2023 a yankin kudu maso gabashin ƙasar.

Gwamnatin Najeriya ta ce ba za ta lamunci da yadda ɗan-tawayen yake kalamai da barazana a kan harkokin Najeriya ba sakaka, yadda yake so ba tare da gwamnatin Finland ta ɗauki mataki a kansa ba.

A kwanan nan ya ayyana dokar zaman-gida ta kwana biyar wadda ya ce za ta fara daga ranar Alhamis 23 ga watan Fabarairu zuwa 28 ga watan na Fabarairu, wanda wannan ne ya sa fargaba a zaukatan mutane a yankin kudu maso gabashin Najeriya kan zaɓukan da za a yi.

Wane ne Simon Epka?

Simon Ekpa dan Najeriya ne da ke da takardar zama ɗan ƙasar Finland wanda ke kiran kansa ɗalibin jagoran 'yan a-ware na haramtacciyar ƙungiyar IPOB mai fafutukar ɓalle yankin da suke kira Biafra a kudu maso gabashi daga Najeriya wato, Nnamdi Kanu, wanda ke tsare.

Ekpa wanda ke zaune a Finland tare da neman farfaɗo da fafutukar 'yan a-waren Biafra na kira ne ga jama'a a yankin kudu maso gabashin Najeriya da su ƙaurace wa zabukan da za a yi a Najeriyar har sai hukumomin ƙasar sun saki Nnamdi Kanu.

A shafinsa na Twitter, Ekpa na bayyana kansa a matsayin mai fafutukar kare ƴancin dan'Adam, ɗan siyasar Finland, kakakin Biafra, lauya da dai sauran muƙamai.