You are here: HomeAfricaBBC2023 09 01Article 1836347

BBC Hausa of Friday, 1 September 2023

Source: BBC

Jadawalin UEFA Conference League: Aston Villa za ta kara da Az Alkamaar

File photo File photo

An raba jaddawalin gasar UEFA Conference League ta bana inda Aston Villa ta samu kanta a rukunin E tare da AZ Alkmaar ta kasar Netherlands da Legia Warsaw ta ƙasar Poland, da kuma Zrinjski Mostar ta ƙasar Bosnia and Herzegovina.

Ga cikakken jadawalin gasar

Rukunin A: Lille, Slovan Bratislava, Olimpija Ljubljana da Ki Klaksvik

Rukunin B: Gent, Maccabi Tel Aviv, Zorya Luhansk da Breioablik

Rukunin C: Dinamo Zagreb, Viktoria Plzen, Astana da Ballkani

Rukunin D: Club Brugge, Bode/Glimt, Besiktas da Lugano

Rukunin E: AZ Alkmaar, Aston Villa, Legia Warsaw da Zrinjski Mostar

Rukunin F: Ferencvaros, Fiorentina, Genk da Cukaricki

Rukunin G: Eintracht Frankfurt, PAOK Thessaloniki, HJK Helsinki da Aberdeen

Rukunin H: Fenerbahce, Ludogorets Razgrad, Spartak Trnava da Nordsjalland

A ranar 29 ga watan Mayu ne za a yi wasan ƙarshe na gasar cin kofin Europa conference League a filin wasan Agia Sofia da ke birnin Athens na ƙasar Girka.

Filin wasan mai ɗaukan mutum 32,000 da ake kira AEK Arena, shi ne filin wasan ƙungiyar AEK Athens.