You are here: HomeAfricaBBC2023 09 01Article 1836311

BBC Hausa of Friday, 1 September 2023

Source: BBC

Iwobi na shirin komawa Fulham

Alex Iwobi (dama) Alex Iwobi (dama)

Fulham ta kulla yarjejeniya da Everton kan farashin dan wasan tsakiya Alex Iwobi.

Dan Najeriya, mai shekaru 27, yanzu zai tafi Landan ne domin a duba lafiyarsa da nufin kammala cinikin kafin a rufe kasuwar musayar 'yan wasa.

Iwobi ya buga wasanni biyu daga cikin ukun da Everton ta buga a gasar Premier ta bana, inda Toffees din har yanzu ba ta samu maki ko daya ba kuma ta zauna daram a kasan teburi.

Rauni ya hana shi buga wasan da Wolves ta doke Everton a gida ranar Asabar.

Ya koma kungiyar ne daga Arsenal a bazarar 2019 kuma ya buga wasanni 123 a gasar, inda ya zura kwallaye shida.