You are here: HomeAfricaBBC2023 07 17Article 1806356

BBC Hausa of Monday, 17 July 2023

Source: BBC

Inter Miami ta gabatar da Messi a gaban magoya bayanta

Lionel Messi Lionel Messi

Inter Miami ta gabatar da kyaftin din tawagar Argentina, Lionel Messi a gaban magoya bayanta a matakin sabon dan kwallonta.

Kungiyar da ke buga gasar kwallon kafar Amurka, MLS ta gabatar da dan kwallon tare da Sergio Busquets a daren Lahadi.

Kimanin mutum 20,000 ne, wadanda suka tsaya a cikin ruwan sama da walƙiya don ganin lokacin da a aka mika wa zakaran Ballon d'Or riga mai lamba 10.

Filin wasan DRV PNK da ke Fort Lauderdale filin wasa ne na wucin gadi na Inter Miami, kuma yana iya daukar mutane 18,000, amma an gina wani babban dandali na wucin gadi don bai wa karin magoya bayan kungiyar daman shiga filin wasan.

Daya daga mamallakin Inter Miami, David Beckham ya bayyana dauko Messi da kungiyar ta yi a matsayin "cikar buri".

A wani takaitaccen jawabi da ya yi cikin harshen Sipaniya, Messi, mai shekaru 36, ya godewa magoya bayansa.

Zai sake taka leda tare da dan wasan tsakiya Sergio Busquets - wanda su ka yi tamaula a Barcelona - wanda kuma ya kulla yarjejeniya da Miami har zuwa karshen kakar 2025.

Messi ya bar Paris St-Germain a karshen kakar 2022-23, bayan da ya zura kwallo 32 a raga a wasa 75 a tsawon shekaru biyu.

Ya yi watsi da tayin da ya samu daga wasu kasashe don ya buga wasa a Amurka - kuma wannan ne karon farko da zai buga wa kulob din da ba na Turai ba.

Ana sa ran Messi zai samu damar buga wa Miami wasa da kungiyar LIGA MX Cruz Azul a ranar 21 ga watan Yuli a wasansu na farko na gasar cin kofin Leagues.