You are here: HomeAfricaBBC2023 08 09Article 1821815

BBC Hausa of Wednesday, 9 August 2023

Source: BBC

Iniesta ya koma kungiyar Emirates

Tsohon dan wasan Barcelona Andres Iniesta Tsohon dan wasan Barcelona Andres Iniesta

Tsohon dan wasan Barcelona Andres Iniesta ya kulla yarjejeniya da kungiyar Emirates Club ta gasar United Arab Emirates Pro League.

Dan kasar Sifaniyan ya bar Vissel Kobe ta kasar Japan a tsakiyar kakar wasannin J-League ranar 1 ga watan Yuli.

Dan wasan mai shekaru 39, ya buga wasa 134 a kulob din na Japan, inda ya lashe Emperor's Cup a shekarar 2019 da kuma Super Cup na Japan a shekarar da ta biyo baya.

Kungiyar Emirates, wacce ta yi nasara a gasar ta UAE a kakar wasan da ta wuce, ta yi wa dan kwallon "maraba'' a shafukanta na sada zumunta.

Iniesta ya koma Japan ne bayan ya shafe shekaru 22 yana taka leda a Barcelona, ​​inda ya lashe kofuna 32 da buga wasa 674.

Ya lashe wasa 133 tare da kasar Sifaniya da cin gasar kofin duniya ta 2010 da kuma gasar kofin nahiyar Turai a 2008 da 2012.

Sabon kulob din nasa zai fara kakar wasan bana da Al-Wasl a ranar 19 ga watan Agusta.