You are here: HomeAfricaBBC2023 08 02Article 1817345

BBC Hausa of Wednesday, 2 August 2023

Source: BBC

Ina sa ran wata rana mijina zai dawo - Matar Dadiyata

Dadiyata ya bache ne a jihar Kaduna a arewacin Najeriya Dadiyata ya bache ne a jihar Kaduna a arewacin Najeriya

Ranar Laraba, 2 ga watan Agusta ake cika shekara huɗu da ɓatan Abubakar Idris, shahararre kuma marubuci a shafukan sada zumunta wanda kuma aka fi sani da Dadiyata.

A watan Agustan 2019 ne aka bi shi har gida a daidai lokacin da ya dawo daga tafiya, inda aka sace shi da motarsa.

Tun sace shi da aka yi daga gidansa ba a sake jin labarinsa ba.

Tun daga lokacin wasu suka zargi hukumar tsaron farin kaya ta DSS da ɗauke shi, sai dai hukumar ta musanta zargin.

A baya an sha samun kiraye-kirayen sakin sa daga 'yan uwa da abokan gwagwarmayar matashin.

"A irin wannan rana ce wasu mutane ɗauke da makamai suka yi garkuwa da Abubakar Idris (Dadiyata) - wanda ya shahara wajen sukar gwamnatin Najeriya a shafukan sada zumunta - a gidansa da ke Kaduna," a cewar Kungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International cikin wani sako a shafinta na Twitter.

Kafin sace shi, Abubakar Dadiyata ya yi fice wajen sukar manufofin gwamnatin Jihar Kano ta lokacin da kuma ta tarayya.

Matarsa Khadija Abubakar Dadiyata ta bayyana wa BBC halin da ta tsinci kanta tun bayan sace mijin nata.

‘’Mun tsinci kanmu cikin halin baƙin-ciki da damuwa sakamakon rashin sanin inda yake, mun shiga mun fita wajen shugabanni duk inda za mu je mu kai kukanmu, mun je mun kai kukanmu’’.

Ta ce ba ta ɗauka za a kawo wannan lokaci mai tsawo haka ba tare da sakin mijin nata ba.

‘’Ban ɗauka abin zai kai kwanaki masu yawa ba, amma yanzu ga shi har shekaaru hudu’’

Yadda rayuwar iyalansa ta kasance tsawon wannan lokaci

Khadija Abubakar ta ce abin sai dai godiyar Allah kawai.

A cewarta, rayuwar waɗanda ke zaune da mazajensu ma a wannan lokaci dauriya kawai suke, ballantana ita da babu mijin a kusa da ita.

"‘Yan uwan mijina da abokansa ne suke taimaka min da 'ya'yana," in ji ta.

Khadija Dadiyata ta ce tsawon shekarun nan hudu kullum takan kwantar wa yaranta biyu hankali da cewa mahaifin nasu tafiya ya yi kuma zai dawo.

‘Ban sani ba ko har yanzu ana neman mijina’

Matar Dadiyata ta shaida wa BBC cewa a halin yanzu ba ta sani ba ko har yanzu hukumomi na neman mijin nata ko kuma sun hakura.

‘’A farko-farkon abin, an nuna mana cewa ana gudanar da bincike, binciken da har yanzu ba mu san halin da ake ciki ba, kuma yanzu babu wanda ya sake yi mana magana kan wannan batu’,’ in ji ta.

Khadija Abubakar ta ce ba ta taɓa ji a ranta cewa ta rabu da mijin nata kenan ba. ‘’Ina fatan wata rana mijina zai dawo gare ni’’.

Ta kuma yi kira ga hukumomi da gwamnatin ƙasar su taimaka wajen ceto mijin nata, saboda a cewarta ‘’na fara tunanin cewa karyar da nake yi wa yarana zai iya yin tasiri idan suka fahimci cewa ƙarya nake yi musu, kar su fara kallo na a matsayin maƙaryaciya’’.

‘’Don girman Allah idan akwai wani taimako da za a iya yi mana na ganin an samo wurin da yake ko wani labari a kan sa, don Allah a taimaka’’.

Wane ne Dadiyata?

Asalin sunansa Abubakar Idris, sunan mahaifinsa Danjuma Yero, mahaifiyarsa kuma Fatima Abubakar.

Ana kiran sa Daddy a gida saboda yana da sunan kakansa na wajen mahaifiyarsa. Abokansa kuma suna kiran sa Dadiyata.

Matashi ne wanda ya yi fice a shafukan sada zumunta musamman ma a Twitter, inda yake da dubunnan mabiya.

Dadiyata malami ne a Jami'ar Tarayya ta Dutsinma da ke jihar Katsina kafin a sace shi.

Cikakken magoyin bayan Kwankwasiyya ne - salon siyasa a Kano - kuma a nan ne ya fi yin suna saboda yawan kare muradun tsohon Gwamnan Kano Rabi'u Musa Kwankwaso da yake yi.

Abubakar mutum ne mai yawan tsokaci a shafukan sada zumunta, inda a wasu lokuta yakan soki ayyukan wasu shugabannin siyasa da masu mulki.

Dadiyata na da mata ɗaya da 'ya'ya mata biyu.

Yadda aka sace Dadiyata

Cikin wata hira da BBC a 2021, matarsa ta ce ya dawo gida ne daga tafiya da misalin karfe 12:30 na dare, a ranar 2 ga watan Agusta.

Daidai lokacin da ya shigo gida da motarsa sai wasu mutane suka biyo shi a baya inda suka kama shi da kokowa suka sanya shi cikin motar tasa suka yi gaba da shi.

Ta ce ta daga labule a lokacin da al'amarin ke faruwa inda ta gansu sanye da takunkumin rufe fuska.

A cikin daren ta yi ƙoƙarin kiran mahaifansa amma ba ta same su ba, sai yayarsa ta samu ta shaida wa halin da ake ciki.

Ita kuma tun da Asuba ta je gidan ta sanar da su halin da ake ciki.

Hakan ya sanya matasa da dama waɗanda suka san shi a shafukan sada zumunta suka fito da maudu'ai da dama kamar #FreeDadiyata da #WhereIsDadiyata? Da dai sauransu domin daga muryarsu da kira ga mahukunta da a gano inda yake.