You are here: HomeAfricaBBC2023 05 30Article 1776845

BBC Hausa of Tuesday, 30 May 2023

Source: BBC

Ina neman afuwa kan wahalhalun da wasu tsare-tsarenmu suka haifar - Buhari

Tsohon shugaba Muhammadu Buahri Tsohon shugaba Muhammadu Buahri

Shugaban Najeriya mai barin gado, Muhammadu Buhari ya ce ya yi iyakar bakin kokarinsa wajen ganin ya sauke nauyin da ya dauka na mulkin kasar, kuma zai ci gaba da yi wa kasar addu’a bayan sauka daga mulki.

Shugaban ya fadi haka ne a jawabin da ya yi wa al’ummar kasar, karo na karshe a matsayin shugaban kasa.

A ranar Litinin 29 ga watan Mayun 2023 ne gwamnatin shugaba Buhari ke zuwa karshe bayan kwashe shekara takwas yana mulki.

Kuma a ranar ce sabuwar gwannati za ta kama aiki inda za a rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasa, bayan lashe zaben da ya yi a watan Fabarairu.

A lokacin da yake bayani kan tattalin arziki, shugaba Buhari ya ce “Tattalin arizikinmu (Najeriya) ya kara zamantowa mai jurewa saboda irin matakan da aka dauka domin ganin cewa bai durkushe ba a lokacin da tattalin arzikin duniya ya shiga mummunan hali.”

Ya kara da cewa “A kokarin inganta tattalin arziki mun dauki matakai masu matukar wahala wadanda yawancinsu suka samar da sakamako mai kyau. Wasu daga cikin matakan sun haifar da wahalhalu, kuma ina mai neman afuwar al’ummar kasa game da hakan. Sai dai mun dauki matakan ne domin amfanin wannan kasa.”

Jawabin na shugaba Buhari ya tabo lamurra da dama, ciki har da kokarinsa na yaki da rashawa.

Shugaba Buhari ya ce “Yan uwana yan Najeriya kun san yadda, har cikin zuciyata nake matukar so na ga na yaki rashawa wanda shi ne ya hana kasar ci gaba. Na yi bakin kokarina wajen ganin an ci nasara duk da irin turjiyar da muka samu wadda da ma mun yi tsammanin hakan.”

“Ina murna kan cewa an samu kwato kudade an dawo da su gida kuma an kwato kadarorin da aka saya da kudin haram”

A batun tsaro shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta yi iyakar bakin kokarinta, inda ta samu nasarar “rage kaifin ayyukan ‘yan bindiga da ta’addanci da fashi da makami da sauran ayyukan barna.”

Buhari ya kuma bukaci al’ummar Najeriya su kasance masu taimaka wa jami’an tsaro ta hanyar lura da abubuwa da ke faruwa a yankunansu domin ganin an dora kan nasarar da gwamnatinsa ta samu.

Ya kuma ce “Har yanzu ina takaicin yadda ake ci gaba da garkuwa da yaranmu. Ina jajanta wa iyaye da abokai da ‘yan uwan wadanda suka rasa rayukansu a wannan harkalla da tashin hankali. Dakarun tsaronmu na aiki babu dare ba rana domin ganin sun karbo wadanda har yanzu ake garkuwa da su.”