You are here: HomeAfricaBBC2023 07 04Article 1797845

BBC Hausa of Tuesday, 4 July 2023

Source: BBC

Ina ne sansanin Jenin, kuma me ya sa rikici ke ta'azzara a yankin?

Hoton alama Hoton alama

Isra'ila ta ƙaddamar da wani gagarumin farmakin soji a Jenin da ke gabar yammacin kogin Jordan da ta mamaye.

Dakarunta na fafatawa ne da rundunar Jenin Brigades, wani rukunin mayaƙa da ya ƙunshi ƙungiyoyin gwagwarmayar Falasɗinawa daban-daban, da ke sansanin ‘yan gudun hijira na birnin.

Ina ne sansanin Jenin? Kuma ya girmansa yake?

Sansanin 'yan gudun hijiran yana cikin birnin Jenin, a yankin arewacin yamma da gabar kogin Jordan da aka mamaye.

Sansanin a cike yake maƙil. Ya kasance gida ga mutane kimanin 14,000, waɗanda ke zaune a wani yanki da bai wuce rabin murabba'in kilomita ba, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Shi kansa birnin Jenin yana da yawan mutane 50,000.

Sansanin kuma yana ɗauke da rundunar Jenin Brigades, wani haɗe-haɗen tarin mayaƙa daga ƙungiyoyin gwagwarmayar Falasɗinawa daban-daban da suka hada da Hamas da kuma Islamic Jihad.

Me aka sani game da tashin hankalin kwanan nan a Jenin?

A cikin 'yan makonnin da suka gabata, tashe-tashen hankula a kewayen Jenin da sansanin na kara ta'azzara.

A ranar 20 ga watan Yuni, an kashe Falasɗinawa bakwai a wani farmaki da Isra'ila ta kai a Jenin, inda aka yi amfani da wani jirgin sama mai saukar angulu.

Washegari ne wasu ‘yan bindigar Hamas biyu suka harbe wasu ‘yan Isra’ila huɗu a gidan mai da kuma wani gidan cin abinci da ke makwabtaka da unguwar Eli mai tazarar kilomita 40 daga kudancin Jenin.

Bayan haka ne ɗaruruwan sojojin Isra’ila ‘yan kaka-gida suka kai farmaki inda suka ƙona gidaje da motoci a garin Turmusaya da ke kusa da garin. An harbe wani Bafalasɗine a wannan tashin hankalin.

A cikin wannan makon, an kashe wasu 'yan tayar da ƙayar bayan Falasdinawa uku daga Jenin a wani harin da aka kai da jirgi mara matuƙi mallakin Isra'ila, bayan da suka kai harin bindiga a wani wurin binciken ababen hawa da ke kusa da birnin.

Ana ganin wannan farmakin na yanzu na ɗaya daga cikin manyan ayyukan da sojojin Isra'ila suka gudanar a yammacin gabar kogin Jordan cikin shekaru da dama.

Mai magana da yawun sojin Isra'ila ya bayyana sansanin a matsayin "matattaran ta'addanci".

Firaministan Falasɗinu Mohammad Shtayyeh ya bayyana harin a matsayin wani sabon yunƙuri na lalata sansanin da kuma tarwatsa mazauna cikinsa.

Me ya sa Jenin ya zama matattarar tashin hankali?

Jenin, na daya daga cikin wuraren da ke gabar yammacin kogin Jordan inda sabbin mayakan Falasdinawa suka mamaye, in ji Paul Adams, wakilin BBC kan harkokin diflomasiyya.

“Waɗannan matasan ‘yan bindigan ba su taɓa sanin shirin zaman lafiya ba,” in ji shi. “Ba su san ta yadda za a bi a warware rikici ta hanyar diflomasiya ba.

"Ba su da kwarin gwiwa kan shugabannin yankin. Don haka suke yaƙar mamaya ta hanyar da suke ganin za su iya."

Mene ne tarihin sansanin Jenin?

An kafa sansanin ne a farkon shekarun 1950 domin tsugunar da Falasdinawa wadanda suka yi gudun hijira a lokacin yakin 1948-49.

An gwabza wannan faɗa ne tsakanin Isra'ila da sojojin Larabawa lokacin da aka kafa ƙasar Isra'ila.

Sansanin ya zama muhimmin fagen daga a lokacin intifada na biyu na Falasdinawa.

A watan Afrilun 2002, sojojin Isra'ila sun ƙaddamar da wani gagarumin farmaki, wanda aka fi sani da yakin Jenin.

Wannan farmaki ne na kwanaki 10 wanda ya biyo bayan harin ƙunar bakin wake da Falasɗinawan suka kai a Isra'ila, wanda yawancinsu suka kasancen mazauna Jenin.

Aƙalla mayaƙa da fararen hulan Falasɗinawa 52, da sojojin Isra'ila 23 ne aka kashe a faɗan.