You are here: HomeAfricaBBC2023 01 11Article 1693616

BBC Hausa of Wednesday, 11 January 2023

Source: BBC

Ina da rikitattun dabaru na doke Man United - Pep Guardiola

Kocin Manchester United Ten Hag da na Manchester City Pep Guardiola Kocin Manchester United Ten Hag da na Manchester City Pep Guardiola

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce yana da wani "birkitaccen tsari" kan yadda zai doke abokiyar hamayyarsu Manchester United a wasan da za su fafata ranar Asabar a Old Trafford.

City za ta buga wasan ne tana matsayi na biyu a teburin Premier League, tazarar maki huɗu kenan tsakaninta da United wadda ke mataki na huɗu.

Guardiola ya yi nasara a wasan hamayyar Manchester tara cikin 17 da ya jagoranci City tun da ya maye gurbin Manuel Pellagrini a 2016 - an doke shi a wasa shida.

Ɗan ƙasar Sifaniyan ya ƙare dukkan kakar wasanin da ya buga na shekara shida a saman United a kan teburin gasar ta Premeir.

Erik ten Hag ne mai horarwar United na huɗu da zai fuskanci Guardiola a wannan tsakanin. Guardiola ya cinye su duka, inda ya doke Ten Hag a wasan ƙarshe da suka buga 6-3 a filin wasa na Etihad a watan Oktoba.

"Ina son na buga wasan da 'yan ƙwallon da ba su buga wasanni da yawa ba saboda ba ni da tunani mai yawa kan doke su, dabara har da birkitacciya," in ji Guardiola.

Sai kuma United ta rasa maki 10 ne kawai cikin wasa 10 da ta buga a Premeir tun daga haɗuwarsu ta ƙarshe kuma ta ci huɗu a jere da ta buga a bay-bayan nan.

Wannan ce bajinta mafi kyau da suka taɓa yi tun watan Maris na 2021.