You are here: HomeAfricaBBC2023 07 25Article 1811909

BBC Hausa of Tuesday, 25 July 2023

Source: BBC

Illoli huɗu na rashin naɗa ministoci kan lokaci

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Lokaci na ƙure wa shugaban Najeriya Bola Tinubu kan wa'adin da kundin tsarin mulki ya ba shi na gabatar da sunayen ministocinsa.

A ranar 29 ga watan Maris ne aka naɗa Bola Tinubu a matsayin shugaban Najeriya bayan lashe zaɓen da ya yi a watan Fabarairun 2023.

Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu, kafin sauka daga mulki ya sanya hannu kan ƙuduri na 23, wanda ya yi gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin Najeriya, inda ya buƙaci shugaban ƙasa da kuma gwamnoni su gabatar da sunayen ministoci ko kwamishinoni cikin kwana 60 bayan shan rantsuwar kama aiki.

Tun makonni biyu da suka gabata ne ake raɗe-raɗin cewa a kowane lokaci Tinubu zai iya gabatar da sunayen ministocin nasa.

A yanzu shugaban na Najeriya ya shafe kwana 57 a kan mulki, bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu.

To sai dai irin wannan jinkiri, ta-bakin masana na da nasa illolin ga ƙasa.

Farfesa Kamilu Sani Fagge, masani a harkar siyasa da ke birnin Kano a Najeriya ya yi wa BBC bayani kan illolin:

Gurguncewar ayyukan gwamnati

"Ministoci su ne wakilan shugaban ƙasa kuma su ne ake ɗora wa alhakin gudanar da al'amuran gwamnati, don haka idan aka yi jinkiri za ka ga an tsayar da ayyukan gwamnati." In ji Farfesa Fagge.

Ya ce a duk lokacin da aka samu jinkiri wajen naɗa ministoci ayyukan gwamnati kan tsaya cik, kasancewar su ne ke da nauyin jagorantar ma'aikatun gwamnati.

A wannan yanayi ragamar tafiyar da lamurran gwamnati kan koma ne a hannun ma'aikatan gwamnati.

Sai dai lamurran sau da dama ba su tafiya yadda suka kamata ganin cewar shugabantar ma'aikatun na gwamnati aiki ne na ƴan siyasa waɗanda shugaban ƙasa ke naɗawa.

Bunƙasa cin hanci da rashawa

Masanin ya ce rashin minsitoci a ma'aikatun gwamnati kan bayar da dama a riƙa yin almundahana kasancewar babu shugaba da zai kwaɓa.

Ya ce "hakan na sanyawa a rinƙa cin kare babu babbaka wajen yin wandaƙa da kudin gwamnati."

Matsin lamba

Farfesa Fagge ya ce rashin miƙa sunan ministoci da wuri kan sanya matsi a kan shugaban ƙasa, wani lamari da kan raba masa hankali.

Ya ƙara da cewa "Za ka ga an hana shugaban ƙasa sakat,"

"Masu faɗa a-ji za su rinƙa matsa lamba wajen ganin an shigar da su ko wani nasu a cikin waɗanda za a bai wa muƙamin."

Wannan a cewa Sani Fagge kan sanya duk hankula su koma kan batun naɗin minitoci a maimakon mayar da hankali wajen tafiyar da lamurran ƙasa.

Tsoma ma'aikatan gwamnati cikin siyasa

Farfesa ya kuma ce rashin ministoci kan sanya ma'aikatan gwamnati su zamo su ne ke gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyan ƴan siyasa.

Kasancewar wajibi ne aikin gwamnati ya ci gaba da gudana, ma'aikatan gwamnati kan gudanar da ayyukan da suka rataya ga ƴan siyasa.

Wannan kan sanya ma'aikatan gwamnati su rinƙa hulɗa da ƴan siyasa, kamar shi shugaban ƙasa.

Ta hakan ne siyasa kan shiga cikin harkar gwamnati.

Ministoci muhimman ginshiƙai ne a ɓangaren zartarswar gwamnati a Najeriya.

Kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada, ministoci za su kasance mashawarta ga shugaban ƙasa, wanda shi ne jagoran ɓangaren na zartaswa na gwamnatin tarayya.