You are here: HomeAfricaBBC2021 05 24Article 1268734

BBC Hausa of Monday, 24 May 2021

Source: BBC

Ibrahim Attahiru: Wa zai maye gurbin babban hasfan sojin Najeriya

Marigayi Laftanar Janar Ibrahim Attahiru, tsohon babban hafsan sojin kasa na Najeriya Marigayi Laftanar Janar Ibrahim Attahiru, tsohon babban hafsan sojin kasa na Najeriya

Bayan rasuwar babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru yanzu hankali ya koma kan wanda zai gaje shi.

Laftanar Janar Attahiru Ibrahim wanda ke jagorantar yaki da masu tayar da kayar baya a Najeriya ya rasu ne tare da sojoji 10 da suka ƙunshi Janar guda uku a hatsarin jirgin sama a jihar Kaduna a ranar Juma'ar da ta gabata.

Attahiru shi ne ya maye gurbin Janar Tukur Buratai a wani yunkurin kawo sauyi kan yaƙi da kungiyar Boko Haram, da kuma rashin tsaro da ake fama da shi a sauran sassan Najeriya.

Kafin ba shi muƙamin babban hafsan sojin kasa na Najeriya shi ne shugaban runduna ta 82 a rundunar sojin ƙasar.

Shugaba Buhari da sauran masu ruwa da tsaki a Najeriya sun bayyana Janar Attahiru a matsayin gwarzo da nuna jarumtaka a ƙoƙarinsa na murƙushe ƙungiyar Boko Haram da 'ƴan bindiga masu fashin daji da suka addabi arewacin Najeriya.

Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum sun soma tsokaci kan wanda zai maye gurbin marigayin a irin wannan lokacin da kasar ke fuskantar ƙalubalen tsaro a sassa daban-daban na ƙasar.

Wasu majiyoyi a fadar shugaban Najeriya sun nuna cewa ba za a ɗauki lokaci mai tsawo ba kafin a naɗa sabon babban hafsan sojin kasa na Najeriyar.

'Buhari ne ke da wuƙa da nama'

Wani babban jami'in soji ya ce akwai wasu matakai da ake la'akari da su wajen naɗin sabbin manyan hafsoshin tsaro.

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari wanda shi ne babban kwamandan askarawan Najeriya shi yake da zaɓin duk wanda yake so watakila ya karɓi shawarar ministan tsaro kan wanda ya dace a naɗa babban hafsan sojin ƙasa.

Jaridar PRNigeria da ke da kusanci da rundunar sojin Najeriya ta ce har an fara tunanin wanda zai gaje shi.

Daga cikin waɗanda ake tunanin za su gaji Janar Attahiru sun haɗa da Manjo Janar Danjuma Ali-Keffi, wanda shi ne kwamandan rundunar sojin kasa da ke Kaduna.

Masana harkokin tsaro da dama na ganin idan har hakan ta faru to kuwa waɗanda ke gaban shi za su yi ritaya.

Hakan na nufin za a yi asarar manyan janar-janar a lokacin da ake matukar buƙatar aikinsu.

Sai dai kuma ba abun mamaki ba ne kauce wa tsarin daɗewa cikin shekarun aiki wurin yin irin wannan naɗi.

Don kuwa a lokuta da dama kasashe kan yi la'akari da ƙwazo da jajircewa da kuma ƙwarewa kan abin da ya shafi tsaro da leƙen asiri wurin zaɓar babban hafsan soja.

Daga cikin manyan sojojin da ke da ƙwarewa kan abin da ya shafi yaƙi da 'ƴan tayar da kayar baya akwai Manjo Janar Ben Ahanotu.

Ahanotu ne ya jagoranci kama tsohon shugaban ƙungiyar Boko Haram Muhammed Yusuf a Maiduguri a shekarar 2009.

Haka kuma akwai Manjo Janar AM Aliyu, wanda ƙwararre ne kan tsaro da leken asiri.

Akwai kuma Manjo Janar Ibrahim Manu Yusuf wanda ya jagoranci rundunar hadakar jami'an tsaro ta Operation Lafiya Dole a arewa maso gabashin Najeriya.

Haka kuma akwai Manjo Janar Faruk Yahaya, wanda yanzu haka ke jagorantar yaƙi da Boko Haram a arewa maso gabasshin Najeriya.

Manjo Janar Faruk ya taba riƙe muƙamin kwamandan rundunar sojin kasa ta matakin farko.

A cikin makon nan ne ake sa ran Shugaba Buhari zai sanar da sabon babban hafsan sojin kasa kuma duk wanda ya samu sai ya zage damtse wajen aiki domin kawo karshen matsalolin tsaro a kasar.