You are here: HomeAfricaBBC2022 12 04Article 1674410

BBC Hausa of Sunday, 4 December 2022

Source: BBC

Iran ta rushe hukumar Hisbah bayan zanga-zanga a kasar

Wasu yan zanga zanga a Iran Wasu yan zanga zanga a Iran

Babban lauyan gwamnatin Iran, Mohammad Jafar Montazeri ya ce hukumomi sun rushe rundunar 'yan Hisbah ta kasar.

An samar da jami'an ne domin tabbatar da bin tsarin sanya tufafi na Musulunci.

Matakin da gwamnatin kasar ta dauka a ranar Lahadi bai fayyace ko wace hukuma ce za ta maye gurbin 'yan Hisbah din.

"Hukumar hisbah din ba ta da alaka da bangaren shari'a kuma an rushe ta", in ji Montazeri.

Kasar na fama da tarzoma mummuna ta kin jinin gwamnati tun bayan da wata matashi mai shekara 22, Mahsa Amini ta rasu a hannun 'yan Hisbar.

An kama ta ne bisa zargin kin daura dan kwalinta ko hijabi yadda ya kamata.

Babban lauyan na gwamnatin Iran din ya kuma ce majalisar dokoki da kuma bangaren shari'a na kasar suna sake nazarin dokokin sanya tufafin.

Tun a shekarar 1983 ne dai aka yi dokar tilasta wa mata sanya hijabi a Iran.

Me matasan Iran ke so bayan shafe makonni suna zanga-zanga?

An shafe makonni a zanga-zanga a faɗin ƙasar Iran, wadda mutuwar wata matashiya ta haddasa.

Tun daga wancan lokaci kuma buƙatun masu zanga-zangar ke ƙara yawa game da abin da matasan ke neman a sauyi a kai.

Abin da ya fara haddasa rikicin shi ne mutuwar Mahsa Amini - matashiyar 'yar ƙabilar Kurdawa wadda ta mutu bayan 'yan sandan addini na Iran sun tsare ta saboda zargin ta da karya dokar rufe gashinsu da hijabi ko ɗan-kwali.

Akasarin masu zanga-zangar mata ne da ke neman sanin dalilin abin da ya kashe ta.

Sun buƙaci bayanai da soke dokar saka hijabi da kuma soke 'yan sandan Hisbah na Iran da ke tabbatar da bin dokar.