BBC Hausa of Sunday, 4 December 2022

Source: BBC

Ingila za ta hadu da Faransa a wasan gabda na kusa da karshe

England players celebrate England players celebrate

Ingila za ta hadu da Faransa a wasan gabda na kusa da karshe bayan ta samu nasara a kan Senegal da ci uku da nema a wasan da suka buga a filin wasa na Al Bayt.

Jordan Henderson ne ya ci wa Ingila kwallon farko a minti na 38 sannan sai kyaftin din tawagar 'Three Lions' watau Harry Kane ya ci wa kasarsa kwallo ta biyu ana gabda tafiya hutun rabin lokaci.

Bukayo Saka ne ya ci kwallo ta uku a minti na 57, kwallon da ya tabbatar wa Ingila cewa za ta kai zagaye na gaba.

A wasan farko na zagaye na biyu da aka buga a ranar Lahadi, Faransa ce ta doke Poland da ci uku da daya.

A lokacin wasan Olivier Giroud ne ya ci kwallon farko inda ya kara tarihi a matsayin dan wasan da yafi kowanne zura kwallo a tawagar maza ta Faransa.

A yanzu ya ci kwallo 52 watau ya shiga gaban Thierry Henry.

Kylian Mbappé ne ya ci wa Faransa kwallo biyu a wasan kuma a yanzu shi ne kan gaba wajen zura kwallo a gasar cin kofin duniya da ake buga wa a Qatar.

Dan kwallon na PSG a yanzu ya ci kwallo biyar kenan a gasar.