You are here: HomeAfricaBBC2023 03 09Article 1728041

BBC Hausa of Thursday, 9 March 2023

Source: BBC

Hatsarin jirgin ƙasa ya kashe aƙalla mutum uku a Legas

Hoto daga wajen hatsarin jirgin kasa da motar bas Hoto daga wajen hatsarin jirgin kasa da motar bas

An tabbatar da mutuwar aƙalla mutum uku, yayin da wasu da dama suka samu rauni lokacin da jirgin ƙasa ya buge wata motar bas da safiyar Alhamis a yankin Ikeja da ke jihar Legas.

Shugaban Hukumar agajin gaggauwa ta ƙasa (NEMA), na yankin kudu maso yammacin Najeriya, Ibrahim Farinloye shi ne ya tabbatar da lamarin.

A baya jami'in ya ce mutum biyu ne, sai dai daga bisani ya ce yawan waɗanda suka mutu ɗin ya ƙaru zuwa uku.

Ya ce "mata biyu ma'aikatan gwamnatin jiha da wani namiji ne suka rasu."

Motar bas ɗin wadda ta gwamnatin jiha ce na ƙoƙarin tsallaka hanyar jirgin ƙasa ta PWD/Sogunle ne a lokacin da jirgin, wanda ya fito daga Abeokuta zuwa cikin birnin Legas ya yi awon-gaba da ita.