You are here: HomeAfricaBBC2023 08 22Article 1829873

BBC Hausa of Tuesday, 22 August 2023

Source: BBC

Harin Ukraine ya lalata jirgin yaƙin Rasha

Hoton alama Hoton alama

Wani jirgin Ukraine mara matuƙi ya kai wa jirgin yakin Rasha mai ɗauke da bam mai cin dogon zango hari tare da lalata shi, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Wani hoto da aka wallafa a kafafen sada zumunta wanda BBC ta tantance ya nuna jirgin ƙirar Tu-22 na ci da wuta a sansaninsu da ke kudancin birnin St Petresburg.

Moscow ta ce wani makami ne aka harbo wa jirgin wanda kuma ya lalata shi baki ɗaya. Ukraine ba ta ce komai ba a kan lamarin.

Jirgin ƙirar Tu-22 na mugun gudu kuma da shi Rasha ke yawan amfani wajen kai hare-hare a biranen Ukraine.

Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce harin da "coper-type UAV" ya kai ne da misalin karfe 10:00 a gogon Moscow na ranar Asabar.

Ya fara ne daga wajen da "jiragen sojoji suke a yankin Novgorod", inda sansanin jiragensu na Solty -2 suke.

"Ɓangaren da ke lura da sararin samaniya sun gano UAV ɗin kuma sun harbe shi da wani ƙaramin makami," in ji ma'aikatar.

"An lalata jirgin sama guda; babu dai wanda ya raunata a yayin harin na 'yan ta'adda."

Sanarwar ta ce wutar da ta tashi a wajen ajiye jiragen an kashe ta cikin gaggawa.

Wani hoto da aka wallafa a shafukan sada zumunta da kuma Telegram ya nuna yadda wutar ta mamaye wani ƙaragin jirgi mai saukar ungulu ƙirar Tu-22. BBC ta tantance hoton ta ga cewa na gaske ne.

Lalata jirgin guda ba zai haifar da wani gagarumin koma baya ba ga jirgin na Moscow, wani mataki da ke nuna Kyiv na ƙara samun ƙarfin kai hari yankunan Rasha.

Kyiv ta kwashe watanni wajen kai gwamman hare-haren jirgin sama kan Moscow, cikin wata tafiya da suke yi mai tsawo da mil daruruwa. Tashar Solty-2 na da nisan kilomita 650 daga iyakar Ukraine.

Jirgin Tu-22 da aka yi amfani da shi a lokacin yaƙin cacar baka da ke amfani da bam, Nato ta yi masa suna da "Backfire" wanda ake matuƙar amfani da su wajen kai wa biranen Ukraine hare-hare.

Jirgin ƙirar zamani na Tu-22M3 na tafiya mai tsawo cikin ƙanƙanin lokaci kuma zai iya ɗaukar makami mai nauyin 24,000 kilogiram ciki har da bam ɗin da ake wurgawa da kuma makami mai linzami

An riƙa amfani da shi a rikicin Syria da Chechnya da Geogia a bayan nan kuma an yi amfani da shi a Ukraine.

A cewar masu shigar da ƙara a Kyiv, harin da Tu-22 ya kai a Dnipro a Janairu ya kashe mutum 30.

Kafafen yaɗa labarai na Rasha sun rawaito wannan harin, sai dai sun musanta cewa ya yi ɓarna.