You are here: HomeAfricaBBC2023 05 15Article 1767617

BBC Hausa of Monday, 15 May 2023

Source: BBC

Har yanzu dakarun Rasha na da karfi sosai a Ukraine - NATO

Hoton alama Hoton alama

Kungiyar tsaro ta NATO ta ce duk da dimbin asarar da sojojin Rasha suka tabka a fagen-daga a Ukraine har yanzu mafi yawan rundunoninta na nan daram.

Babban Kwamandan kungiyar a Turai Janar Christopher Cavoli shi ne ya bayyana haka a yayin taron tsaro a yankin Baltic.

Kwamandan ya ce a yanzu Rasha tana da dakaru a cikin Ukraine fiye da a farkon mamayar da ta yi wa makwabciyar tata a watan Fabarairu na shekarar da ta gabata.

Babban Kwamandan kungiyar tsaron ta NATO a Turai ya ce akwai bukatar a duba rundunar sojin Rashar ta kowane bangare ba wai ta kasa ba kadai.

Janar Cavoli Ba’amurke yana wannan magana ne a yayin wannan taro na tsaro a yankin Baltic, inda ya bayar da wannan sheda da ke nuna cewa sojin na Rasha na nan daram duk da irin illar da aka yi musu a fagen-daga wadda ya ce ba a tantama.

Kwamandan ya ce rundunar sojin ruwa ta Rashar tana nan kusan kamar ba abin da ya nakasta ta, yayin da sojojinta na sama kuwa kusan jiragen yaki dari daya suka rasa amma har yanzu suna nan da wajen dubu daya kuma karfin dakarun ta sama da kuma intanet na nan daram.

Ya kara da cewa maimakon ma a samu raguwar sojojin na Rasha a yanzu sun ma fi na farkon lokacin da kasar ta mamayi makwabciyar tata a watan Fabarairu na bara.

Janar Cavoli, wanda har-wa-yau shi ne ke jagorantar dakarun Amurka a Turai ya yi gargadin cewa duk da irin asarar sojin da Rasha ta tafka a Ukraine , NATO za ta dauki lokaci kafin ta murkushe Rasha ta kowane bangare a nan gaba.

Shi kuwa Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine wanda ke kara-kaina tsakanin manyan kasashe kawaye domin samun gudummawa a yakin ya nuna cewa a cikin wannan shekara za su ci galaba a kan Rashar.

Mista Zelensky na magana ne a Jamus lokacin da ya kai ziyarar godiya ga shugaban gwamnati Olaf Scholz kan sabon tallafin soji da ya kai na dala miliyan dubu uku da Jamus din ta bai wa Ukraine;

Ya ce, ‘’yanzu ne lokacin da ya kamata mu kawo karshen wannan yaki a wannan shekara. A wannan shekara za mu iya murkushe masu mamayar.''

Wani babban masanin harkar tsaro wanda ya nemi a boye sunansa ya sheda wa taron cewa makamai masu linzami masu cin dogon zango da Birtaniya ta bai wa Ukraine hadi da karin harsasai da Amurka za ta kara wa kasar, za su iya taimakawa sosai wajen ganin Ukraine ta tilasta wa sojojin mamayar na Rasha baya.