You are here: HomeAfricaBBC2023 01 11Article 1693640

BBC Hausa of Wednesday, 11 January 2023

Source: BBC

Halin da na shiga bayan kisan da ɗan sanda ya yi wa ɗana

Hoton alama Hoton alama

Mutuwar Muhammad Jawwad dalibin firamare sakamakon harbin 'yan sanda a wani yankin birnin Katsina na ci gaba da haifar da damuwa tsakanin 'yan uwa da wasu al'umomin Jihar.

Iyayen yaron mai shekaru 9 a duniya sun bayyana yanayi na damuwa da baƙin ciki da suka shiga na tsawon kwanaki, bayan harbe-harben da ya halaka ɗansu da kuma raunata wasu mutane uku.

Mahaifin yaron, Yusuf Rufa'i mazaunin birnin Katsina ya shaidawa BBC cewa suna cikin yanayi na tashin hankali da jimamin ɗan su, da ya rasu yana da karancin shekaru ba tare da aikata wani laifi ba.

Mutuwar yaron dai a ranar ɗaya ga watan Janairun 2023, ya tada hankula inda wasu ke ganin akwai sakaci jami’an tsaro.

Me ya kai ga harbi?

Lamarin dai ya auku ne yayin da wata hatsaniya ta kaure a lokacin da wasu 'yan sanda suka je kama wani matashi, DJ, wato mai harkar sanya kaɗe-kaɗen shakatawa a wajen biki da sauran taruka.

Isar jami'an tsaron wurin ke da wuya, sai ɗaya daga cikinsu ya harba bindigarsa, a kokarin dakatar da DJn daga kaɗe-kaɗe.

Wannan harbi da ɗan sanda ya yi ya faɗa kan mutane da ke wajen da ake kaɗe-kaɗen da kuma wanda hanya ce ta kai shi ya ratsa ta wajen taron.

Mutum uku suka jikkata daga harbin, yayinda wani yaro ɗan firamare ya gamu da ajalinsa.

'Na kasa daina kukan ɗa na'

Jama'a dai na cigaba da bibiyar batun zargin harbin da ake yiwa jami'in ɗan sandan.

Mahaifin yaron ya shaidawa BBC cewa, baya ga ɗan sa da ya rasu cikin waɗanda aka jikkata a akwai yaro ɗan shekara 20 mai suna Abdulganiyu Yusuf, harsashi ya cire masa 'yan ƴatsu biyu.

Sai kuma harsashin da ya sami wani yaro mai suna Ahmed Shu'aibu a wuya ɗan shekara 10.

Muhammadu Rabi'u kuma harsashi ya same shi a ciki, inda nan take ana iya hango kayan hanjinsa.

'Yan sanda sun yi gaggawar kai shi asibiti domin ceto ransa.

A cewar Yusuf, tsautsayi yaronsa na hanyar dawo wa daga makarantar allo abin ya riske shi, harsashin ya same shi a baya.

"Harsashin ya lalata ma sa laka har zuwa cikinsa, wanda Allah bai yi ya fita ba har aka yi jana'izarsa.

"Su sauran mutane uku da harsashin ya same su, suna can kwance a asibiti cikin yanayin tausayi".

Malam Yusuf ya ce ɗansa mai fara'a ne da ladabi wanda kowa ke yabawa da hankalinsa.

Ya ce hawan-jini ya kama mahaifiyarsa, akwai kusanci sosai tsakanisa da mahaifiyarsa inda yake yawaita taimaka mata.

  Me jami'an tsaro ke cewa?

Kakakin 'yan sanda Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da faruwar al'amarin.

SP Gambo, ya ce lamarin ya auku ne bayan wani kiran gaggawa da aka yiwa jami'an tsaro a yankin Sabuwar Unguwa.

Sai dai suna isa yankin sai wasu matasa suka yi kokarin kai wa jami'ansu hari, a cewarsa wannan yanayi ne ya tursasawa jami'an harba bindiga domin tarwatsa su.

Ya ce an lallata motar 'yan sanda guda da kuma baburansu biyu a hatsaniyar.

SP Gambo ya ce sun mika ta'azziyarsu ga iyayen yaron da ajali ya riske shi sakamakon wannan lamari, kuma suna ci gaba da aiwatar da bincike.