BBC Hausa of Thursday, 20 April 2023
Source: BBC
Manchester City da Bayern Munich sun tashi 1-1 a wasa na biyu a zagayen quarter finals a Champions League ranar Laraba a Jamus.
City ta ci kwallon ta hannun Erling Haaland a minti na 12 da komawa zagaye na biyu a Allianze Arena.
Kwallo na 12 da ya zura a raga a Champions League a bana, shine na daya a yawan cin kwallaye a gasar a kakar nan.
Haaland ya yi kan-kan-kan da Ruud van Nistelrooy dan wasan Premier League da ya ci kwallo 12 a Champions League a kakar 2002/03.
Haka kuma tun farko Haaland ya barar da fenariti a wasan na ranar Laraba, karon farko daga 16 da ya buga a baya, tun bayan da ya barar a Borussia Dortmund da Union Berlin a Afirilun 2021.
Saura minti takwas a tashi daga wasan Bayern ta zare daya ta hannun Joshua Kimmich a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Da wannan sakamakon City ta kai zagayen daf da karshe da cin kwallo 4-1 gida da waje ta fitar da Bayern daga gasar bana.
Pep Guardiola ya zama na uku da ya ci wasa na 100 a Champions League a matakin koci, wanda ya ja ragamar Barcelona da Bayern Municyh da yanzu a City.
Bayern Munich ta yi canji biyu ko ta sauya sakamakon, inda Sadio Mane ya canji Leroy Sane, wadanda suka tafa hannu.
Ranar 11 ga watan Afirilu a Eihad, bayan da aka ci Bayern 3-0 an bai wa hammata iska tsakanin Mane da Sane, inda wasu rahotanni suka ce dan wasan Senegal ya naushi Sane.
Daya canjin da Bayern ta yi a lokaci guda shine wanda Joao Cancelo ya maye gurbin Alphonso Davies.
Wannan shine karon farko da aka tashi 1-1 tsakain kungoyin biyu, inda City ta yi nasara a hudu, Bayern Munich ta ci wasa uku daga takwas da suka kara a Champions League.
Wasa takwas tsakanin Bayern da Manchester City:
Champions League Laraba 11 ga watan Maris



