You are here: HomeAfricaBBC2023 09 17Article 1845887

BBC Hausa of Sunday, 17 September 2023

Source: BBC

Haaland ya ci kwallo bakwai a wasa biyar a Premier a bana

Erling Braut Haaland, dan wasan Man City Erling Braut Haaland, dan wasan Man City

Manchester City ta je ta doke West Ham 3-1 a wasan mako na biyar a gasar Premier League ranar Asabar.

James Ward-Prowse ne ya fara ci wa West Ham kwallo a minti na 36, sai Jeremy Doku ya farke wa City kwallon.

Daga baya ne Bernardo Silva ya kara na biyu, sannan Erling Haaland ya ci na uku a wasan kwallo na bakwai da ya zura a raga kawo yanzu.

Haaland ya fara da cin kwallo a karawa da Burnley da City ta ci 3-0 a wasan farko na kakar nan ranar 11 ga watan Agusta.

Ya kuma ci kwallo na uku ranar 27 ga watan Agusta a fafatawar da City ta je ta ci Sheffield 2-1, sannan ya zura kwallo uku rigis a ragar Fulham ranar 2 ga watan Satumba.

Wasa na biyar a jere da City ta ci a Premier League a kakar nan, wadda ta taba yin bajintar nasara shida a jere karkashin Pep Guardiola a kakar 2016/17.

Nathan Ake ya shiga wasan daga baya, karo na 200 kenan a Premier League.

City tana matakin farko a kan teburin Premier League da maki 15, West Ham kuwa mai maki 10 tana ta.

Ga jerin wasannin da City ta lashe a bana kawo yanzu:

Premier League Juma'a 11 ga watan Agusta


  • Burnley 0 - 3 Man City

Premier League Asabar 19 ga watan Agusta


  • Man City 1 - 0 Newcastle

Premier League Lahadi 27 ga watan Agusta


  • Sheff Utd 1 - 2 Man City

Premier League Asabar 2 ga watan Satumba


  • Man City 5 - 1 Fulham

Premier League Asabar 16 ga watan Satumba


  • West Ham 1 - 3 Man City