You are here: HomeAfricaBBC2023 01 17Article 1696967

BBC Hausa of Tuesday, 17 January 2023

Source: BBC

Gwamnatin Kano ta kori 'yan mata biyu daga gidan marayu kan zargin tayar da husuma

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje

Hukumomi a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya sun kori wasu 'yan mata daga gidan marayu na gwamnatin jihar.

Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne saboda 'yan matan ba sa bin ƙa'idar zaman gidan tare da ƙoƙarin tayar da husuma tsakanin marayu da ma’aikata.

Sai dai marayun sun ce wasu ma’aikatan gidan ne ke cin zarafinsu ta hanyar ƙoƙarin yin lalata da wasu daga cikinsu.

Ma’aikatar harkokin mata da walwalar al‘ummar ta jihar Kano, ta ce ta kori ‘yan matan biyu daga gidan marayun na Nasarawa ne saboda rashin kiyaye ka’idoji da dokokin zaman gidan.

Sai dai waɗannan ‘yan mata sun ce saboda sun kwarmata lalatar da ake zargin wani ma’aikacin gidan ne ya sa aka kore su, kamar yadda ɗaya daga cikinsu ta shaida wa BBC

Ta ce ''saboda yana da mabuɗin sito a hannansa, yana ganin kamar shi ke da iko da gidan gaba ɗaya, sai muka je muka gaya wa shugabar gidan, daga baya sai ta zo ta ce ai mun yi masa ƙazafi, daga sai suka rubuta takarda suka kai wa Kwamishina, ita kuma ta bayar da umarnin da a rubuta takarda wai an kore mu, daga baya aka zo aka kira mu aka yi mana wa'azi, cewa mu yadda da ƙaddara mai kyau da marar kyau''

Daga nan sai a ka sanar da su cewa gwamna ya bayar da umarni a kore su daga gidan tun da za su janyo masa matsala kamar yadda ta shaida wa BBC.

Ta ƙara da cewa ''mun ɗauki matakin bayyana abin da ma'aikacin gidan ke yi wa 'yan matan da ke gidan ne, saboda 'yan matan da yake lalata da su 'yan uwanmu ne, dan haka bai makata mu yi shiru ba''

Dan haka a cewarsu bai makata a ajiye ma'aikaci ba amma kuma ya riƙa cin amanar yara da gwamnati.

Daga ƙarshe 'yan matan sun yi kira ga gwamnati da ta shiga cikin lamarin tare da taimaka wa wajen samar musu da wurin zama.

Haka kuma 'yan matan sun ƙaryata batun zargin da ake yi musu na tunzura sauran yara da kuma fita daga gidan kuma ba sa dawowa sai lokacin da suka ga dama, domin kuwa a cewarsu suna zaman lafiya da sauran yaran.

To sai dai kwamishinar ma’aikatar mata da ke lura da gidan marayun Hajiya Zara’u Muhammad Umar ta ce da farko sun yi yunƙurin daukar tsattsauran mataki a kan waɗanda ake zargin amma sai aka kafa wani kwamiti, don a yiwa kowanne ɓangare adalci.

Ta da farko ta bayar da umarni cewa ma'aikacin ya bar aiki, a gidan daga baya kuma bayan an kama kwamiti wanda ya ƙunshi 'yansa bayan da kwamitin ya gudanar da binciken an gano cewa ma'aikacin ba shi da hannu a duka zarge-zargen da ake yi masa dan haka kwamitin ya bayar da shawar cewa kar a zalunce shi.

Ta kuma ce daya daga cikin 'yan matan ma har dukan yaran dake cikin gidan take yi.

Kwamishinar ta ce dama can doka ba ta ba su damar ajiye irin waɗannan manyan 'yan mata ba, kawai dai sun yi hgaka ne dan tausaywa.

Su dai ‘yan matan biyu da gwamnatin ta sallama sun shaida wa BBc cewa an basu naira 40,000 domin su nemi gidan haya, amma sun ce kuɗin ba zai isa su sami gida ba.