You are here: HomeAfricaBBC2021 05 12Article 1259599

BBC Hausa of Wednesday, 12 May 2021

Source: BBC

Gwamnatin Habasha ta musanta kisan kiyashi a Tigray

Rahoton ta ya bayyana yadda sojojin Habasha da na Eritrea suka kashe farar hula sama da dari Rahoton ta ya bayyana yadda sojojin Habasha da na Eritrea suka kashe farar hula sama da dari

Gwamnatin Habasha ta ce binciken da ta gudanar kan zargin kisan kiyashin da aka yi a birnin Axum a watan Nuwambar bara, ya tabbatar da cewa 'yan tawaye 93 aka kashe ba farar hula ba.

Wannan bayani da ofishin mai shigar da kara na gwamnati ya fitar, ya ci karo da wanda hukumar kare hakkin dan adam ta kasar ta fitar.

Rahoton ta ya bayyana yadda sojojin Habasha da na Eritrea suka kashe farar hula sama da dari.

Ganau sun shaidawa kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International da kuma BBC yadda aka kashe daruruwan mutane cikin kwanaki biyu.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun ce dukkan bangarorin da ke fada da juna sun aikata muggan laifuka.

Rikici tsakanin dakarun gwamnatin tarayya na Habasha, da kuma na yankin Tigray ya jefa yankin cikin hali na rashin zaman lafiya, tare da tilastawa dubban mutane tserewa daga kasar zuwa Sudan mai makoftaka.

An shafe watanni ana rikici, wanda ya dagula al'amura a ƙasar da ta fi kowace yawan mutane a yankin Gabashin Afrika.

Rikicin siyasa da na neman mulki da kuma neman kawo sauyi a siyasar ƙasar na daga cikin abubuwa da dama da suka yi sanadiyyar rikicin.