You are here: HomeAfricaBBC2021 03 30Article 1219444

BBC Hausa of Tuesday, 30 March 2021

Source: BBC

Gwamnatin Bolsonaro na Brazil na cikin rudani

Shugaban Brazil Jair Bolsonaro Shugaban Brazil Jair Bolsonaro

Dole ta sanya shugaban Brazil Jair Bolsonaro, yin gagarumin gyaran fuska a majalisar ministocinsa, sakamakon ajiye mukamin da ministan harkokin waje da kuma na tsaro suka yi, daya bayan daya a jere.

Minista harkokin wajen, Ernesto Araújo, mai matukar ikon fadi a ji a gwamnatin, ya samu kansa cikin matsin lamba sakamakon gazawarsa ta sama wa kasar ta Brazil karin allurar rigakafin korona.

To amma shi kuwa ministan tsaro wanda ba a yi tsammanin saukar tasa ba, saukarsa ta sa masu nazari na ganin shugaban kasar mai ra'ayin rikau na fuskantar matsalar siyasa mafi girma a gwamnatinsa.

A wata rana da za a ce mafi rikita- rikitar siyasa a Brazil, shugaban kasar, Jair Bolsonaro mai tsananin ra'ayin 'yan mazan jiya ya rasa wasu manyan jiga-jigan abokan tafiyarsa da ke rike da muhimman mukamai a gwamnatinsa.

Na farko dai shi ne ministansa na harkokin waje, Ernesto Araujo, mai jawo ce-ce-ku-ce, wanda shi ma kamar shugaban mutum ne mai tsattsauran ra'ayin rikau, wanda ya ajiye aikin bayan da ya gamu da matsin lamba da suka ba kakkautawa daga 'yan majalisar dokoki a karshen mako a kan martaninsa game da batun korona, da kuma abin da ake gani bata matsayin Brazil a duniya.

Mista Araujo ya kasance mai musanta illolin sauyin yanayi a ko da yaushe.

Kuma kusan a kullum yana cikin rikici da sabanin ra'ayi da China, babba kuma dadaddiyar abokiyar huldar tattalin arziki da kasuwanci ta kasarsa Brazil.

Sai dai ajiye mukamin nasa wanda daman da dama sun yi tsammaninsa, ya samu rakiyar saukar takwaransa na ma'aikatar tsaro, Fernando Azevedo e Silva wanda shi kuma ko kadan ba a yi tsammani ba.

Wannan gibi da aka samu kwatsam a gwamnatin, ya bude kofar, gagarumin gyaran fuska a tafiyar, inda Shugaba Bolsonaron ya sauya ministoci shida ke nan akalla jumulla da wadancan biyu da suka sauka.

Sauye-sauyen sun kuma sa ana rade-radi da yada jita-jita a kafafen yada labarai cewa, wata rikita-rikitar da babban sabani na nan na kunno kai a tsakanin manyan hafsoshin sojin kasar uku, abin da ya sa ake ganin akwai matsala ta gaske a gwamnatin ta Bolsonaro.

Wannan rikici da koma- baya da gwamnatin ta samu kanta a ciki yanzu, sun fito ne yayin da farin jinin shugaban kasar ke dusashewa a 'yan makonnin nan, a kan yadda ya tunkari batun annobar korona, musamman ma bayan sake bullowar babban abokin hamayyarsa, tsohon shugaban kasar ta Brazil Luiz Inacio Lula da Silva.