You are here: HomeAfricaBBC2023 07 29Article 1814750

BBC Hausa of Saturday, 29 July 2023

Source: BBC

Gwamnati Gombe ta ce ta kwace iko da dukkan burtalan jihar

Nigeria map | File foto Nigeria map | File foto

Gwamnatin jahar Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya, ta bayyana cewa za ta mayar da dukkan burtalan da ke cikin jihar karkashin kulawarta.

Gwamnatin ta ce ta kafa wani kwamiti da ya kunshi shugabannin manoma da makiyaya da sarakunan gargajiya da masana muhalli da sauran su, domin duba wannan shirin.

Wannan mataki na gwamnatin na da nasaba da irin halin da aka shiga na yawan samun rikici tsakanin manoma da makiyaya.

Gwamnan jihar, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya shaida wa BBC cewa wajibi ne a yi maganin wannan matsala ta yawan rikici tsakanin manoma da makiyaya.

Ya ce, ’’ Mun kafa wannan kwamiti ne saboda abin da muka lura da shi na yawan samun rikici tsakanin manoma da makiyaya kuma kusan za a ce batun burtali na daga cikin abin da ke janyo wannan rikici.”

Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce karuwar jama’a ma ta sa daga makiyaya har manoman kowa na da tasa bukatar inda neman abinci ke karuwa haka bukatar ciyar da dabbobi ta karu.

Gwamnan na Gombe ya ce ada ba a fiye da samun rikici tsakanin manoma da makiyaya ba saboda jama’a ba su kai yawan na yanzu ba, kuma dabbobi ma suna da burtalan da suke bi ba sa bi ta gonakin manoma.

Amma a yanzu saboda yawan jama’a duk an cike burtalan da gine gine abin da ke sa makiyaya kan bi ta gonakin manoma ke nan da dabbobinsu, in ji shi.

Ya ce, su ma manoma da nasu laifin saboda suna cinye hanyoyin da aka yi wa dabbobi su wuce da gonakinsu, hakan kuma kan sa dole dabbobi su bi ta gonakinsu.

A baya bayan nan dai yawan sare dazuka da gurgozowar hamada sun janwo makiyaya na barin dazuka su shigo cikin gari lamarin da ke janyo rikici tsakaninsu da manoma.

To ko wannan kwamitin da gwamnatin jihar ta Gombe ta kafa zai yi tasiri wajen dakile rikicin da ake tsakanin manoma da makiyaya? Abin da jama’ a suke jira su gani ke nan.