You are here: HomeAfricaBBC2023 09 12Article 1842989

BBC Hausa of Tuesday, 12 September 2023

Source: BBC

Guardiola zai ja ragamar wasan City da West Ham bayan jinya

Pep Guardiola Pep Guardiola

Ana sa ran Pep Guardiola zai koma Ingila ranar Laraba, domin jan ragamar wasan da Manchester City za ta kara da West Ham a gasar Premier League.

Ranar Asabar 16 ga watan Satumba City za ta ziyarci West Ham, domin fafatawa a wasan mako na biyar a babbar gasar tamaula ta Ingila.

City tana matakin farko a kan teburi da maki 12, bayan cin dukkan wasa hudu da fara kakar nan, yayin da West Ham mai maki 10 take ta hudu.

Guardiola, wanda ya yi jinya sakamakon ciwon baya, bai ja ragamar City wasan Premier da ta doke Sheffield United da Fulham a cikin watan Agusta ba.

Mataimakin Guardiola, Juanma Lillo ne ya ja ragamar wasan da City ta je ta ci Sheffield United 2-1 da wanda ta caskara Everton 5-1 a Etihad.

Daga ranar Laraba 'yan wasa da dama za su fara komawa kungiyoyinsu, bayan da suka buga wa tawagoginsu tamaula.

Guardiola ya lashe Premier League da FA Cup da Champions League a karon farko a City a bara.

Haka kuma dan kasar Sifaniya ya dauki Uefa Super Cup a dai kakar da ta wuce, bayan doke Sevilla 5-4 a bugun fenariti, bayan da suka tashi 1-1 a Athens.