You are here: HomeAfricaBBC2023 02 14Article 1714364

BBC Hausa of Tuesday, 14 February 2023

Source: BBC

Guardiola ya nemi afuwar Gerrard bayan subul da baka

Pep Guardiola ya nemi afuwa ga Steven Gerrard (hagu) Pep Guardiola ya nemi afuwa ga Steven Gerrard (hagu)

Pep Guardiola ya nemi afuwa ga Steven Gerrard kan kalaman da ya yi na zamewar tsohon kyaftin din Liverpool a wasa da Chelsea da ya fadi.

A lokacin da yake kare Manchester City kan tuhuma sama da 100 ta Financial Fair Play, ya kwatanta batun da tsautsayin da Liverpool ta yi rashin nasara 2-0 hannun Chelsea a 2013-14.

Dalilin da Liverpool ta kasa daukar Premier League, City ta lashe a lokacin.

''Ina neman afuwar Steven Gerrard kan kalaman da na yi da ba su da ce ba,'' in ji Guardiola.

''Ya kwan da sanin yadda nake kaunarsa da sana'arsa da bajintar da ya yi wa kasarsa, wadda nake zaune a ciki nake gudanar da aiki.''

Zamewar da Gerrard ya yi, wanda bai taba lashe Premier League ba a tarihin tamaularsa, ya sa Dembe Ba ya ci Liverpool a Anfield a Afirilun 2014.

Ita kuwa City ta ci wasanta a lokacin daga nan ta ci karawa biyu da suka rage, sannan ta lashe Premier League.

Manuel Pellegrini ne kociyan City' a lokacin daga baya Guardiola ya karbi aikin a 2016.

''Ban sani ba ko mune muka yi sanadin da Steven Gerrard ya zame ya fadi,'' abin da Guardiola ya fada kenan a makon jiya.

Guardiola ya gyara kalaman da ya yi a lokacin ganawa da 'yan jarida kafin wasan Arsenal da City ranar Laraba a gasar Premier a Etihad.

''Na ji kunyar kaima da batutuwan da na fada, domin Gerrard bai cancanci hakan ba.''

''Na nemi afuwa a wajensa, amma na zabi na fada gaban kowa kuma a wannan lokacin.''

''Ina mai bayar da hakuri ga shi da mai dakinsa Alex da iyalansa, saboda bai kamata ba abin da na fada.''