You are here: HomeAfricaBBC2023 08 22Article 1829849

BBC Hausa of Tuesday, 22 August 2023

Source: BBC

Guardiola ba zai ja ragamar City wasa biyu ba a Premier

Pep Guardiola Pep Guardiola

Kocin Manchester City, Pep Guardiola ba zai ja ragamar wasa biyu a gasar Premier da kungiyarsa za ta buga, bayan da aka yi masa tiyata sakamakon ciwon baya.

Guardiola, mai shekaru 52, ya sha fama da abin da City ta kira "ciwo mai tsanani" kuma ya tafi Barcelona don yin karamin tiyata amma cikin "gaggawa''.

City za ta je Sheffield United ranar Lahadi kuma za ta karbi bakuncin Fulham a ranar 2 ga watan Satumba a filin wasan Etihad.

Ana sa ran Guardiola zai dawo bakin aiki bayan an dawo hutun wasannin kasa da kasa.

Mataimakin kocin Juanma Lillo ne zai karbi ja ragamar a lokacin da Guardiola ba ya nan.

Guardiola ya jagoranci kungiyar zuwa lashe gasar Premier da kofin FA da kuma gasar cin kofin zakarun Turai na farko a kakar bara.

City ce ta biyu a teburin Premier a farkon wannan kakar, inda ta ke da maki shida, bayan da ta doke Burnley da Newcastle a wasa biyu na farko.

Haka kuma ta lashe kofin Uefa Super Cup bayan da ta doke Sevilla da ci 5-4 a bugun fenariti a Athens a makon jiya.