You are here: HomeAfricaBBC2023 09 17Article 1845863

BBC Hausa of Sunday, 17 September 2023

Source: BBC

Greenwood ya fara buga wa Getafe kwallo wanda ya bar United

Mason Greenwood Mason Greenwood

Mason Greenwood ya fara buga kwallo a karon farko bayan wata 20 a karawar La Liga da kungiyarsa Getafe ta ci Osasuna 3-2 a wasan mako na biyar.

Rabon da ɗan kwallon Manchester United ya taka leda tun cikin Janairun 2022, bayan da aka tsare shi kan zargin cin zarafi.

Cikin tuhumar da aka yi wa ɗan wasan mai shekara 21 har da ƙoƙarin yin lalata da kuma wasu munanan ayyukan, waɗanda aka soke su ranar 2 ga watan Fabrairun 2023.

Getafe ta ɗauki aron ɗan wasan, bayan watanni shida da aka yi ana bincikensa a United, inda kungiyar Old Trafford ta ce hakan zai bai wa ɗan kwallon damar komawa kan ganiya.

Lokacin da Greenword zai shiga fafatawar an yi ta masa tafi daga magoya bayan Getafe, amma kuma wasu daga magoya bayan Osasuna ba su yi wata murna ba.

Wata kwallo da Greenword ya buga wadda ta nufi raga aka doke ta zuwa kwana, ita ce da aka buga kungiyar ta zura na uku a raga, inda kungiyar ta koma cikin 'yan 10 farko a La Liga.

A Sifaniya an caccaki Getafe daga wasu kungiyoyin yaƙi da cin zarafi, bayan da ta yanke shawarar za ta ɗauki aron ɗan kwallon.

Getafe ta kare kanta na dalilin ɗaukar ɗan wasan tawagar Ingila da cewar an wanke shi da soso da sabula, shi ya sa ta ɗauki aron matashin.