You are here: HomeAfricaBBC2023 09 30Article 1854044

BBC Hausa of Saturday, 30 September 2023

Source: BBC

Gobara ta kashe sama da mutum 100 a wajen wani biki a Iraƙi

Hoto daga wurin gobarar Hoto daga wurin gobarar

Sama da mutane 100 ne suka mutu yayin da wasu sama da 150 suka jikkata bayan tashin wata gobara a wajen wani ɗaurin aure a arewacin Iraqi.

Kafar yaɗa labarai ta ƙasar ra rawaito jimi’an hukumar tsaro ta Civil Defence na cewa wutar ta tashi ne yayin da ake gudanar da bikin a wani ɗakin taro dake lardin Hamdaniyya.

Daruruwan mutane ne suka halarci bikin da aka yi a lardin Nineveh, kafin wutar ta tashi a ranar Talata da daddare.

Babu dai wanda ya san sababin tashin wutar, amma rahotannin farko sun ce ta tashi ne bayan tartsatsin wutar da ake kunnawa amarya da ango.

Har yanzu ba a kai ga tabbatarwa ba idan ango da amaryar ba sa cikin waɗanda suka mutu ko suka jikkata.

Amma rahotanni a cikin gida na cewa suma tuni sun mutu tare da sauran, amma daga baya kamfanin dillancin labarai na ƙasar Nina ya rawaito cewa ba su mutu ba amma suna cikin waɗanda suka jikkata.

Wani hoto da Nina ya wallafa ya nuna gwamman masu aikin kashe wuta na ta fama, yayin da wasu hotunan ke nuna ƙonannun kayayyakin da suka kone a dakin taron

Rahotanni sun ce an ƙawata ɗakin da kayayyakin da ke saurin kamawa da wuta, kuma sun taimaka wajen habbakar wutar.

"Wutar ta kai ga rushewar wani ɓangare na ginin ɗakin taron sakamakon ƙawata shi da aka yi da abubuwa masu saurin kamawa da wuta, kayan gini ne masu araha waɗanda ke ƙonewa cikin gaggawa," in ji daraktar hukumar tsaro ta civil defence.

Rufin ceilling ɗin dakin ne ya fado ya danne mutane da dama in ji kamfanin dillancin labarai.

Shaidu sun ce da misalin ƙarfe 10 da 45 daidai da 7 da 45 agogon GMT wutar ta tashi.

Mataimakin shugaban Nineveh Hassan Al-Alla1 ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an tabbatar da mutuwar mutum 113, sama da 150 kuma sun raunata.

An kai waɗanda suka jikkata asibitoci daban-daban da ke yankin Nineveh.

Adadin waɗanda suka mutu ka iya ƙaruwa a nan gaba.

A babban asibitin dake Hamdaniya, wanda ke gabashin yakin Mosul, gwamman mutane ne ke tururuwar ba da agajin jini ga waɗanda suka jikkata.

Firaiministan Iraqi ya wallafa a ashinsa na X cewa ya shaida wa jami'ai "a yi gaggawar samar da kayan agaji ga waɗanda gobarar ta rutsa da su."