You are here: HomeAfricaBBC2023 02 06Article 1709243

BBC Hausa of Monday, 6 February 2023

Source: BBC

Girgizar ƙasar Turkiyya: Ya waɗanda suka tsira suka ji?

Hoton gidajen da suka rushe Hoton gidajen da suka rushe

Da misalin ƙarfe 04:17 agogon Turkiyya a lokacin da Erdem ke bacci a gidansa da ke Gaziantep ya ji yana girgiza.

"Ban taɓa jin wani abu irin wannan ba tsawon shekara 40 da na yi a nan," in ji shi.

"Muna nan muna girgiza kusan sau uku da ƙarfi, kamar jariri a cikin gidansa."

Mutane sun tafi zuwa motocinsu domin su gudu daga gine-ginen da suka ruguje.

"Ina tunanin babu ko mutum guda da ke cikin gidansa a Gaziantep a halin yanzu," in ji Erdem.

Sama da kilomita 209 a kudancin ƙasar, a Adana, Nilufer Aslan ta cire rai kan cewa ita da iyalanta za su rasu a lokacin da ƙasa ta girgiza hawa na biyar na ginin da suke zaune.

"Ban taɓa ganin wani abu irin wannan ba a rayuwata. Mun rinƙa girgiza tsawon minti guda," in ji ta.

"[Na shaida wa iyalina] "An samu girgizar ƙasa, aƙalla bari mu mutu tare a wuri guda'....Abin da kawai ya zo mani a rai ke nan."

A lokacin da girgizar ta tsagaita, Aslan sai ta gudu waje - "Ban iya ɗaukar komai tare da ni ba, Ina tsaye a waje da silifas" - inda ta gano cewa gine-gine huɗu da suka zagayeta duk sun rushe.

A Diyarbakir, mai nisan kilomita 482 daga gabashi, mutane da ke kan titi sun garzaya domin aikin ceto.

"Ana ta ihu a ko ina," kamar yadda wani mutum mai shekara 30 ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

"Na soma amfani da hannuwana domin cire duwatsu. Ni da abokaina mun ciro waɗanda suka ci rauni, amma ba a daina ihu ba, sai masu ceto suka je."

A wani wuri da ke birnin, Muhittin Orakci ya ce mutum bakwai cikin iyalansa ɓaraguzai sun danne su.

"Akwai ƴar uwata da ƴayanta uku," kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP. "Haka kuma tare da mijinta, da sirinkinta da sirikarta."

A Syria kuwa, akwai gine-gine masu ɗumbin yawa da suka rushe a Aleppo, da ke da nisan tafiyar sa'o'i biyu daga aihanhin wurin da lamarin ya fi ƙamari..

Daraktan kiwon lafiya Ziad Hage Taha ya bayyana cewa mutanen da suka ji rauni "na ta isowa dayawa," bayan wannan bala'i.

Özgül Konakçı mai shekara 25 wanda ke zaune a Malatya da ke Turkiyya, ya bayyana cewa abubuwan da suka biyo baya da kuma yanayin sanyin da ake ciki ya ƙara ƙazanta lamura.

"Ana cikin matuƙar sanyi a halin yanzu," kamar yadda ta shaida wa sashen BBC Turkiyya.

"Kowa na kan titi, mutane sun shiga ɗimuwa kan abin da za su yi. A gaban idonmu, tagogin wani gini suka tarwatse biyo bayan abin da ya faru."

Sakamakon girgizar ƙasar da ta faru da misalin 10:24 agogon GMT na kasarm wani mai riƙe kemara na gidan talabijin na A Haber an gan shi yana gudu a lokacin da gini ke rugujewa a Malatya, kamar yadda aka ji a bayan fage.

"A lokacin da muke ɓaraguzan domin ɗaukar bidiyon yadda ake aikin nema da ceto, sai aka ji ƙararraki sau biyu masu ƙarfi," in ji ɗan jarida Yuksel Akalan.

"Ginin da kuka gani a hannun hagu naya rushe gaba ɗaya. Akwai ƙura mai yawa. Akwai wani mazaunin yankin da ke tafe wanda ƙura ta biɗe shi. Wata mahaifiya na ɗauke yaranta."

Ozgul Konacki, mai shekara 25 daga Malatya ta yi magana a lokacin da take jiran an uwanta a waje, bayan ta ga gine-gine a kusa da ita da suka rushe.

"Wasu sun so su koma zuwa gidajensu domin akwai tsananin sanyi," in ji ta.

Ismail Al Abdullah- wanda mai aikin ceto ne daga ƙungiyar ayyukan jin ƙai ta Syria mai suna White Helmets- na ta aiki a Sarmada, da ke kusa da iyaka da Turkiyya, inda yake ta aikin ceto.

"Akwai gine-gine a birane da dama da ƙauyuka a arewa maso yammacin Syria da suka rushe sakamakon wannan girgizar ƙasar," in ji shi.