You are here: HomeAfricaBBC2023 02 13Article 1713530

BBC Hausa of Monday, 13 February 2023

Source: BBC

Ghana ta nada Hughton sabon kociyanta

Chris Hughton Chris Hughton

Tawagar kwallon kafa ta Ghana ta nada, Chris Hughton a matakin sabon kociyanta.

Tsohon wanda ya horar da Brighton, mai shekara 64 yana aiki a matakin mai bayar da shawara ga kocin Black Stars tun daga Fabrairun 2022.

Ya maye gurbin Otto Addo, wanda ya ajiye aikin, bayan da Ghana ta yi ta karshe a rukuni na shida da cin wasa daya a gasar kofin duniya a Qatar.

Wannan shi ne aikin farko da Hughton zai horar da tamaula tun bayan da Nottingham Forest ta koreshi a Satumbar 2021.

Ya ja ragamar Newcastle da Birmingham da Norwich da yin kaka biyar a Brighton, wadda ya kai Premier League daga Championship.

George Boateng da Mas-Ud Didi Dramani za su ci gaba da aikin mataimakan koci a tawagar ta Ghana.