You are here: HomeAfricaBBC2023 07 25Article 1811903

BBC Hausa of Tuesday, 25 July 2023

Source: BBC

Gasar cin kofin duniya: Philippines ta doke New Zealand mai masaukin baki

Tawagar kwallon kafa ta Philippines ta doke ta New Zealand da ci 1-0 Tawagar kwallon kafa ta Philippines ta doke ta New Zealand da ci 1-0

Tawagar kwallon kafa ta Philippines ta doke ta New Zealand da ci 1-0 a gasar cin kofin duniya ranar Talata.

Kwallon farko da Sarina Bolden ta zura a raga ya girgiza masu masaukin baki New Zealand, wadanda suka kasa anfani da damar sa suka samu na yunkurin kai wa zagaye gaba.

Wannan shi ne karon farko da phillipines ke buga gasar cin kofin duniya ta mata.

'Yan wasan Philippines sun yi murna bayan tashi daga karawar, yayin da wadanda ke benci da ma'aikatan tawagar suka fantsama cikin filin wasa, bayan tashi daga karawar .

A halin da ake ciki New Zealand, wadda ta yi nasara a kan Norway ranar farko, na bukatar cin wasan gaba, domin kai wa zagaye na biyu.

Kawo yanzu rukunin farko na nufin sai New Zealand ta ci Switzerland don kai wa zagayen gaba a karon farko.