You are here: HomeAfricaBBC2023 07 28Article 1814171

BBC Hausa of Friday, 28 July 2023

Source: BBC

Gasar cin kofin duniya: Ingila ta sanya kafa ɗaya a zagaye na biyu

Yan wasan Ingila Yan wasan Ingila

Ingila na dab da tsallakawa zuwa zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya ta mata bayan da ta yi nasarar doke Denmark 1-0- ko da yake ta yi rashin babbar 'yar wasan tsakiya Keira Walsh ta dalilin rauni.

Lauren James ta fito da kanta ne a fagen wasan duniya da ta ci kwallo mai ban sha'awa mintuna shida kacal da fara wasan da aka buga a filin wasan birnin Sydney.

Denmark ta ci gaba da neman farkewa kuma ta kusa samu lokacin da Amalie Vangsgaard wadda ta ci China a minti na 90 - ta kai wani hari amma ta bugi karfen raga.

Ingila na fama da karancin kwararrun 'yan wasa a tsakiya, inda Jordan Nobbs ta buga wasanni 71 tun lokacin da ta fara buga wasa a 2013, amma wacce za ta iya maye gurbin Walsh kai-tsaye Laura Coombs ta buga wasa sau shida ne kacal tun 2015 - ciki har da wasan da ta maye gurbinta da Denmark.

Ingila za ta tsallake zuwa zagaye na biyu idan har China ta kasa doke Haiti a daya wasan na rukunin D, yayin da Denmark za ta kara da Haiti a wasan karshe na rukunin kuma za ta iya tsallakawa idan ta yi nasara kuma sauran sakamakon rukunin suka tafi yadda ta ke so.