You are here: HomeAfricaBBC2023 08 01Article 1816559

BBC Hausa of Tuesday, 1 August 2023

Source: BBC

Fulham za ta dauki Demarai Gray daga Everton

Demarai Gray Demarai Gray

Fulham tana tattaunawa da dan kwallon tawagar Jamaica, Demarai Gray, daga Everton.

Gray mai shekara 27, ya koma kungiyar da ke Goodison Park daga Bayer Leverkusen kan fam miliyan 1.7 a 2021, wanda ya yi mata wasa 75 da cin kwallo 12.

Crystal Palace,da kungiyar Turkiya Besiktas da wasu daga Saudiyya na son daukar Gray.

BBC ta fahimci cewar Fulham na son daukar Gray domin ta kara karfin kungiyar, don fuskantar kakar bana da za a fara cikin Agustan 2023.

Gray, tsohon dan kwallon Leicester City ya koma yin atisaye, bayan da ya fafata a gasar Concacaf Gold Cup.

Fulham tana da gurbi bayan da Manor Solomon ya koma Tottenham, sannan Dan James ya sake komawa Leeds United.

Kawo yanzu Fulham ta dauki Raul Jimenez daga Wolverhampton da Calvin Bassey daga Ajax a bana.

Wasu rahotanni na cewar Fulham ta kulla yarjejeniyar sayen dan wasan Juventus mai tsaron baya, Luca Pellegrini.