You are here: HomeAfricaBBC2023 08 14Article 1824827

BBC Hausa of Monday, 14 August 2023

Source: BBC

Fred ya kammala komawa Fenerbahce

Fred Fred

Dan wasan Manchester United, Fred ya kammala komawa Fenerbahce ta Turkiya.

Dan kwallon tawagar Brazil, wanda ya koma United daga Shakhtar Donetsk kan fam miliyan 47 a 2018, ya kawo karshen zamansa a Old Trafford.

Ana cewar United za ta samu fam miliyan 10 da karin fam miliyan 4.31 karin tsarabe-tsarabe.

An sanar da Fred cewar da kyar idan za a yi amfani da shi a United karkashin Erik ten Hag a kakar nan..

Kungiyar Galatasaray da Fulham mai buga Premier League, sun so daukar dan kwallon.

Ya buga wa United wasa 56 a kakar da ta wuce da cin kwallo shida a kakar da kungiyar ta yi ta uku da samun gurbin shiga gasar Champions League a bana.

Jimilla ya buga wa United wasa 139 da cin kwallo takwas da bayar da bakwai aka zura a raga.