You are here: HomeAfricaBBC2023 07 26Article 1812782

BBC Hausa of Wednesday, 26 July 2023

Source: BBC

Fitacciyar mawaƙiyar ƙasar Ireland da ta musulunta, Sinéad O'Connor ta rasu

Sinéad O'Connor ta rasu tana da shekara 56 Sinéad O'Connor ta rasu tana da shekara 56

Mawaƙiya 'yar ƙasar Ireland kuma 'yar fafutuka Sinéad O'Connor ta rasu tana da shekara 56.

Wata sanarwa da dangin mawaƙiyar suka fitar ta ce: "cikin ɗumbin takaici muke sanar da ku game da cikawar abar ƙaunarmu Sinéad.

"Dangi da ƙawayenta sun kaɗu kuma sun roƙi a mutunta 'yancinsu na keɓancewa a wannan mawuyacin lokaci."

Ta shahara ne da kundin waƙarta mai taken Nothing Compares 2 U, wadda ta fitar a 1990, inda ta yi tashe a matsayin lamba ta ɗaya a faɗin duniya.

Firaministan Ireland Leo Varadkar ta miƙa saƙon ta'aziyya kan mutuwar mawaƙiyar, inda ya ce kaɗe-kaɗenta "sun samu masoya a faɗin duniya kuma baiwarta ba ta da ta biyu kuma ta fi ƙarfin kwatance".

Mawaƙiyar, wadda ake jin amonta game da batutuwan da suka shafi rayuwar jama'a da siyasa, ta wallafa kundin waƙoƙi guda goma a rayuwarta.

Kundin waƙoƙinta na farko mai taken The Lion and the Cobra ya fito ne a 1987, inda ya shiga sahun fitattun waƙoƙi guda 40 a Birtaniya da Amurka.

Kundinta na biyu mai taken I Do Not Want What I Haven't Got, wanda ya ƙunshi fitacciyar waƙar Nothing Compares 2 U, ya yi tashe a matsayi na ɗaya.

Ɗan mawaƙiyar 'yar asalin birnin Dublin da ake kira Shane mai shekara 17 ya rasu bara, kwanaki bayan an ba da rahoton ɓatansa.

Da take bayani a shafinta na sada zumunta bayan mutuwarsa, Sinéad ta ce ya yanke "shawarar kawo ƙarshen gwagwarmayarsa a doron duniya" kuma ta roƙi "kada wani ya yi koyi da shi".

Ta karɓi addinin Musulunci a 2018, inda ya canza sunanta zuwa Shuhada', amma ta ci gaba da aiki da sunanta na yanka.

A 1992, ɗaya daga cikin al'amura mafi fice a rayuwar sana'arta ya faru ne lokacin da ta yaga wani hoton Fafaroma John Paul na II a cikin wani shirin talbijin na Amurka, inda aka gayyace ta.

Bayan wani shirin raye-raye na waƙar War ta Bob Marley, ta kalli kyamara ta ce "a tashi a yi faɗa da ainihin maƙiya", abin da ake ɗauka a matsayin wani matakin nuna bijirewa ga Cocin Katolika.

Lamarin dai ya yi sanadin haramta sanya waƙoƙinta daga kafar talbijin ta NBC kuma an yi zanga-zangar nuna adawa da ita a Amurka.

"Ba na nadamar abin da na yi. Ya ƙayatar," ta faɗa a wata zantawa da jaridr the New York Times a 2021.