You are here: HomeAfricaBBC2023 03 30Article 1740761

BBC Hausa of Thursday, 30 March 2023

Source: BBC

Fifa ta soke gasar kofin duniya ta matasa da za a yi a Indonesia

Za a fara wasannin ne cikin kasa da watanni biyu Za a fara wasannin ne cikin kasa da watanni biyu

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta soke karbar bakuncin gasar kofin duniya ta ‘yan kasa da shekara 20 da Indonesia ya kamata ta gudanar a bana.

Kasa da wata biyu ya kamata a fara wasannin.

Hakan ya biyo bayan dakatar da bikin raba jadawalin wasannin tun ranar Juma’a da ya kamata a yi a Bali.

Hukumar kwallon kafa ta Indonesia ta ce an tilasta wa Fifa ta soke gasar daga kasar, bayan da gwamnan Bali, Wayan Koster yaki karbar bakuncin tawagar Israel.

Tun farko an tsara buga gasar kofin duniya ta matasa a Indonesia daga 20 ga watan Mayu zuwa 11 ga watan Yuni.

Ita dai Indonesia ba ta da wata yarjejeniyar diplomasiya da Israel.

Kwanaki ma aka gudanar da zanga-zanga kan cewar ya kamata a hana Israel shiga wasannin, domin goyon bayan Palestine

Tun cikin shekarar 2021, Indonesia ya kamata ta gudanar da wasannin, amma bullar cutar korona ya sa aka dage gasar.

Lokacin da aka bai wa Indonesia izinin karbar bakuncin gasar matasa, Peru ce ta biyu.

Fifa ta dage sai Indonesia ta gudanar da wasannin duk kalubalantar kasar da ake ta yi.

A cikin watan Oktoba mutum 135 suka mutu, sakamakon turmutsitsi a sitadiya a wani wasan hamayya tsakanin kungiyoyin tamaular kasar.