You are here: HomeAfricaBBC2023 08 22Article 1829840

BBC Hausa of Tuesday, 22 August 2023

Source: BBC

Faransa ta bai wa Thierry Henry kocin 'yan kasa da shekara 21

Thierry Henry Thierry Henry

An nada tsohon dan wasan Faransa, Thierry Henry a matakin kocin ‘yan kasa da shekara 21 a kasar kan kwantiragin shekaru biyu.

Gwarzon dan wasan Arsenal, wanda ya taimakawa Faransa lashe gasar cin kofin duniya a gida a shekarar 1998, ya gaji Sylvain Ripoli.

Henry, mai shekaru 46, ya ja ragamar wasa biyu a matsayin mataimakin koci a Belgium, kuma ya jagoranci Monaco da Montreal Impact.

Zai jagoranci tawagar Faransa 'Yan shekaru 23 a gasar Olympics ta Paris da za a yi 2024, wanda hukumar kwallon kafa ta Faransa (FFF) ta bayyana a matsayin "babban manufa".

Henry kuma zai jagoranci ‘yan kasa da shekara 21 a neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai a shekarar 2025.