You are here: HomeAfricaBBC2023 08 21Article 1829102

BBC Hausa of Monday, 21 August 2023

Source: BBC

Everton ta yi tir da cin zarafin da aka yiwa 'yan wasanta biyu

Amadou Onana dan wasan Everton (tsakiya) Amadou Onana dan wasan Everton (tsakiya)

Everton ta yi tur da kalaman wariya da cin zarafi da Amadou Onana ya fuskanta bayan rashin nasarar da kungiyar ta yi a wasanta da Aston Villa da ci 4-0 a ranar Lahadi.

Dan wasan tsakiya Onana, mai shekara 22, ya bayyana wani sakon wariyar launin fata da aka yi masa a shafukan sada zumunta.

A makon da ya gabata Everton ta yi tur da cin zarafin da aka yi wa dan wasanta Neal Maupay, wanda aka yi wa a shafukan sada zumunta, sakamakon rashin nasara da kungiyar ta yi a hannun Fulham da ci 1-0 a Premier League.

Everton ta kara da cewa tana gudanar da bincike don gano wadanda ke da hannu a ciki lamarin.

Kungiyar ta kara da cewar za ta taimaka wa ‘yan sanda da duk wani binciken da suke yi.