You are here: HomeAfricaBBC2023 12 11Article 1896719

BBC Hausa of Monday, 11 December 2023

Source: BBC

Everton ta ci wasa na uku a jere bayan doke Chelsea a Premier

Yan wasan Everton a cikin murna Yan wasan Everton a cikin murna

Everton ta yi nasarar cin wasa na uku a jere a Premier League a karon farko tun bayan 2021, bayan da ta doke Chelsea 2-0 a Goodison Park.

Kungiyoyin sun buga wasan mako na 16 a babbar gasar tamaula ta Ingila da suka kara ranar Lahadi.

Sun buga zagayen farko ba ci, amma bayan da suka koma zagaye na biyu ne Everton wadda aka kwashe mata maki 10 ta zura biyu a ragar Chelsea.

An hukunta Everton ne, bayan da aka sameta da karya dokar kasuwancin kungiya.

Abdoulaye Doucoure ne ya fara cin kwallo daga baya Lewis Dobbin, wanda ya shiga wasan canji ya kara na biyu daf da lokaci zai cika.

Wasa na bakwai kenan a Premier League da aka doke Chelsea a bana karkashin Mauricio Pocehettino.

Tun bayan da Everton ta yi rashin nasara a gida da ci 3-0 a hannun Manchester United, kungiyar ta ci karawa uku kenan.

Everton ta je ta ci Nottingham Forest 1-0 ranar 2 ga watan Disamba, sannan ta casa Newcastle 3-0 ranar 7 ga watan Disamba da wanda ta ci Chelsea 2-0.

Everton za ta je gidan Burnley a wasa na gaba ranar 16 ga watan Disamba.