You are here: HomeAfricaBBC2023 07 25Article 1811945

BBC Hausa of Tuesday, 25 July 2023

Source: BBC

Everton ta ɗauki aron Arnaut Danjuma daga Villareal

Arnaut Danjuma Arnaut Danjuma

Everton ta kammala ɗaukar aron Arnaut Danjuma daga Villarreal.

Ɗan wasan tawagar Netherlands ya amince da kunshin yarjejeniyar buga wa Everton wasa a Janairu, amma sai ya koma Tottenham, bayan da aka yi lattin kammala cinikinsa.

Mai shekara 26, ya buga wa Tottenham karawa shida daga baya ya koma Sifaniya da taka leda a babbar gasar ƙasar.

Danjuma ya ce bai amince ya koma Tottenham ba a watan Janairu bayan da ba tabbas kan mai horar da kungiyar kan halin da ta faɗa.

Everton ta kori Frank Lampard daga aiki ranar 23 ga watan Janairu, sannan ta naɗa Sean Dyche mako ɗaya tsakani, saura kwana ɗaya a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ta Turai a lokacin.

Danjuma shi ne na biyu da Dyche ya ɗauka a bana a Everton, bayan Ashley Young.

Danjuma ya buga wa tawagar Netherlands karawa shida, yana cikin 'yan wasan da Liverpool ta ci Villareal a daf da karshe a 2021-22 a Champions League.

Wannan ce kungiya ta uku da zai buga wa tamaula a Ingila, bayan Bournemouth da ya yi a 2019 daga nan ya koma yin wasannin La Liga a 2021.

Everton za ta fara buga wasan farko a kakar Premier League ta bana a gida da Fulham ranar Asabar 12 ga watan Agusta.