You are here: HomeAfricaBBC2023 09 21Article 1848638

BBC Hausa of Thursday, 21 September 2023

Source: BBC

Everton na bincike kan cin zarafin da aka yi wa ɗan wasan Arsenal

Hoton Everton Hoton Everton

Everton ta ce tana aiki tare da 'yan sandan Merseyside don gudanar da bincike kan wani rahoton cin zarafi na wariyar launin fata da aka yi wa ɗan wasan Arsenal.

Lamarin ya faru ne mintuna 15 bayan fara wasan da Everton ta sha kashi a hannun Gunners da ci 1-0 a Goodison Park ranar Lahadi.

A watan Agusta, Everton ta ce za ta ba da haɗin kai a binciken ƴan sanda kan kalaman wariyar launin fatar da aka yi wa ɗan wasanta na tsakiya ɗan ƙasar Belgium Amadou Onana.

A farkon wannan watan, kulob ɗin ya yi Allah-wadai da cin zarafin da aka yi wa ɗan wasan Faransa Neal Maupay a shafukan sada zumunta bayan ta sha kashi a hannun Fulham da ci 1-0 a ranar farko na kakar wasanni ta bana.