You are here: HomeAfricaBBC2023 08 11Article 1823240

BBC Hausa of Friday, 11 August 2023

Source: BBC

Enrique na fatan PSG za ta cimma matsaya da Mbappe

Kylian Mbappe Kylian Mbappe

Kociyan Paris St-Germain, Luis Enrique na fatan kungiyar za ta cimma matsaya da Kylian Mbappe, sannan za ta kammala ɗaukar Ousmane Dembele.

Ɗan kwallon Faransan ba ya yin atisaye da PSG, bayan da ya sanar cewar ba zai tsawaita kwantiraginsa ba da za ta kare a karshen kakar bana.

PSG na son sayar da Mbappe, maimakon ta bar shi ya tafi ba tare da ta samun kuɗi a kan ɗan kwallon ba.

''Ina fatan kungiyar da ɗan wasan za su cimma matsaya da za ta amfani juna.'' in ji tsohon kociyan Barcelona.

Ya kamata Mbappe ya bar PSG a karshen kakar 2021/22, amma sai ya ƙara tsawaitata zuwa kaka biyu da cewar za a iya ƙara masa shekara ɗaya.

Amma yanzu mai shekara 24 ya sanar da kungiyar cewar ba ya fatan ƙara tsawaita zamansa a PSG, wanda ake cewa Real Madrid yake son komawa.

PSG ba ta je atisayen tunkarar kakar bana da Mbappe ba da ta gudanar a Asia.

Bai amince ya tattauna da wakilan Al Hilal ba, waɗanda ke son sayen shi kan fam miliyan 259, domin ya buga gasar Saudiyya.

PSG za ta fara Ligue 1 ta bana da karawa da Lorient ranar Asabar, amma ba a fayyace makomar Mbappe da Neymar da kuma Marco Verratti ba.

Kociyan ya faɗa cewa ''Har yanzu Dembele bai zama ɗan wasan Paris St Germain ba.''