You are here: HomeAfricaBBC2023 03 10Article 1728635

BBC Hausa of Friday, 10 March 2023

Source: BBC

Elliott ya shiga mataki na biyu a shirin sayar da Man United

Filin wasan Manchester United Filin wasan Manchester United

Kamfanin zuba jari mai suna Elliott Investment Management ya shiga mata na biyu a shirin sayar da Manchester United.

Wakilan kamfanin Amurka sun kalli wasan da United ta doke Real Betis 4-1 a Old Trafford a gasar Europa League ranar Alhamis.

Shi kamfanin ba yana kokarin sayen United bane, sai dai zai taimakawa masu son sayen kungiyar ko kuma iyalan Glazer idan sun yanke shawarar ci gaba da gudanar da United.

A cikin watan Nuwamba, iyalan Glazer suka ce suna duba hanyar watakila su sayar da Manchester United.