You are here: HomeAfricaBBC2023 08 14Article 1824824

BBC Hausa of Monday, 14 August 2023

Source: BBC

Eder Militao zai yi jinya mai tsawo a Real Madrid kamar Courtois

Mai tsaron bayan Real Madrid, Eder Militao ya ji rauni a gasar Madrid da Athletic Bilbao Mai tsaron bayan Real Madrid, Eder Militao ya ji rauni a gasar Madrid da Athletic Bilbao

Mai tsaron bayan Real Madrid, Eder Militao ya ji rauni ranar Asabar a wasan farko a La Liga da Real Madrid ta ci Athletic Bilbao 2-0.

Dan kwallon tawagar Brazil, mai shekara 25, shi ne na biyu a Real Madrid da ya ji rauni bayan Thibaut Courtois ke jinya tun daga ranar Alhamis.

An sauya Militao a karawar ta La Liga, bayan raunin da ya ji a gwiwar kafarsa.

Real Madrid ta sanar cewar likitoci za su yi wa dan kwallon tiyata, daga nan za a fayyace ranar da zai koma taka leda.

Sabon dan wasan da Real ta dauka a bana, Jude Bellingham ne ya fara ci mata kwallon farko ranar Asabar, wanda ta dauka daga Borussia Dortmund.

Raunin da Militao ya ji, ya bar koci, Carlo Ancelotti da masu tsaron baya daga tsakiya masu lafiya da suka hada da David Alaba da Antonio Rudiger da kuma Nacho.