You are here: HomeAfricaBBC2021 06 01Article 1275382

BBC Hausa of Tuesday, 1 June 2021

Source: BBC

EFCC ta jefa ma'aikatan bankunan Najeriya cikin ruɗani kan bayyana kadarori

Abdulrasheed Bawa, shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa, shugaban EFCC

Ma'aikatan banki a Najeriya na fuskantar matsin lamba daga hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC bayan ta tilasta masu bayyana ƙadarorin da suka mallaka.

Sanarwar da hukumar ta aika wa BBC ta ce wa'adin da ta ba ma'aikatan Bankunan zai cika a ranar 1 ga watan Yuni.

Hukumar ta ba bankunan wa'adin ne bayan ganawar da shugabanta Abdulrasheed Bawa ya yi da shugaba Muhammadu Buhari a watan Maris inda ya buƙaci ma'aikatan Bankuna su gabatar da fom da ke bayyana ƙadarorin da suka mallaka kafin 1 ga watan Yuni.

EFCC ta ce matakin wani ɓangare ne na aiwatar da tanadin dokar ma'aikatan Banki, da sauransu daga dokar bayyana ƙadarori ta 1986.

"Sashe na 1 na dokar ya wajabta wa ko wane ma'aikacin banki ya gabatar da cikakken bayani game da ƙadarorinsa lokacin da aka ɗauke shi aiki, kuma ya ci gaba da gabatarwa duk shekara."

"Dokar ta yi tanadin hukuncin ɗaurin shekara 10 ga duk wanda ya saɓa, kamar yadda aka bayyana a sashe na bakwai."

"Kuma duk wanda ya saɓa za a yanke masa hukunci tare da ƙwace ƙadarorinsa zuwa ga asusun Gwamnatin Tarayya," in ji EFCC.

Ana ganin dai wannan matakin zai ja hankali tare da tayar da ƙura a Najeriya. Kuma kamar yadda EFCC ta bayyana, ta san cewa wasu ƴan ƙasar za su ƙalubalanci hukumar kan ikon da take da shi na gabatar da umarnin.

Yaƙi da rashawa na cikin alƙawurran da shugaba Muhammadu Buhari ya yi tun a yaƙin neman zaɓensa. Kuma bayyana ƙadarorin jami'an gwamnati na daga cikin matakan shugaban.

A yayin da yanzu wa'adin na EFCC ke cika, ana ganin matakin zai jefa bankuna cikin ruɗani da fargaba musamman game da makomar bankunan da kuma kwastamominsu.

Irin wannan matakin ne Babban Bankin Najeriya ya taɓa ɗauka wanda ya kai ga mutuwar wasu bankuna a Najeriya tare da haɗe wasunsu wuri guda.

Wasu shugabannin Bankunan kuma sun ƙare ne a hannun EFCC, da ta gabatar da su a kotu aka yanke masu hukuncin ɗauri a gidan yari.

Me zai faru bayan cikar wa'adin?

Babu tabbas ko EFCC za ta tsawaita wa'adin ko kuma hukumar za ta ɗaga wa ma'aikatan bankin ƙafa.

Ko kuma EFCC za ta shiga farautar ma'aikatan Bankunan da suka ƙi ba ta haɗin kai.

Sai dai sanarwar da EFCC ta fitar ta ce duk da ta san za ta fuskanci tirjiya amma ta jaddada cewa shugaban hukumar na nan kan bakarsa, "Abin da muke cewa shi ne 1 ga watan Yuni za mu buƙaci fom ɗin bayyana ƙadarori."